Wutar Arewa: Kwankwaso Ya Kawo Mafita ga Gwamnonin Jihohi

Wutar Arewa: Kwankwaso Ya Kawo Mafita ga Gwamnonin Jihohi

  • Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya nuna takaici kan yadda ake cigaba da zama cikin duhu a sassan Arewacin Najeriya
  • Kwankwaso ya ce dole a dauki matakin kawo sauyi a kan yadda jihohi ke samar da wuta kamar yadda Kano ta dauki mataki
  • A yanzu haka dai an shafe kwanaki takwas cikin duhu a Arewa bayan lalacewar wutar lantarki a ranar Litinin da ta wuce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi magana kan matsalar lantarki da ta shafi Arewacin Najeriya.

Rabi'u Kwankwaso ya bukaci gwamnoni su fara neman hanyoyin da za su fara samar da lantarki a jihohi.

Kara karanta wannan

Kwanaki 8 a duhu: Yadda rashin wuta ke durƙusar da kasuwanci da sana'o'i a Arewa

Kwankwaso
Kwankwaso ya bukaci samar da lantarki a jihohi. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro maganganun da Rabi'u Kwankwaso ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya koka kan rashin wuta a Arewa

Sanata Rabi'u Kwankwaso ya nuna damuwa kan yadda aka shiga duhu na tsawon kwanaki takwas a Arewacin Najeriya.

Mafi yawan jihohin Arewa sun shiga duhu ne a sanadiyyar lalacewar layin wutar lantarki da ke jihar Benue.

Magana kan tsadar man fetur

Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa al'umma sun kara shiga wahala a Arewa saboda karin kudin man fetur da aka yi.

A cewar Kwankwaso, tsadar man fetur da dizil sun tilastawa kamfanoni da ma'aikatu rufewa a Arewacin Najeriya.

Sakon Kwankwaso ga gwamnoni

Sanata Kwankwaso ya ce mafita a kan lantarki ita ce gwamnoni su fara samar da wutar lantarki a jihohinsu.

Kara karanta wannan

Ana bakin kokari, TCN ya fadi lokacin dawowar hasken lantarki a Arewa

Kwankwaso ya bayyana cewa Allah ya albarkaci Najeriya da hanyoyin samar da lantarki kuma ya kamata a amfana da su.

Ya kara da cewa a yanzu haka suna ƙoƙarin samar da wutar lantarki daga dam din ruwa na Tiga da Challawa a jihar Kano.

TCN ya yi magana kan lantarkin Arewa

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin rarraba lantarki na kasa (TCN) ya yi magana kan yadda wuta za ta cigaba da kasancewa a Arewa.

TCN ya ce akwai yiwuwar cigaba da samun matsalar wutar lantarki a Arewacin Najeriya saboda wasu dalilan tsaro da yankin ke fama da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng