"Na Yi Shekara 3 da Rabi a cikin Mahaifiyata": Tsohon Gwamna Ya Fadi Abin Al'ajabi

"Na Yi Shekara 3 da Rabi a cikin Mahaifiyata": Tsohon Gwamna Ya Fadi Abin Al'ajabi

  • Tsohon gwamnan jihar Ogun ya ba ƴan Najeriya labarin abin al'ajabin da ya faru da shi kafin ya zo duniya
  • Ibikunle Amosun ya bayyana cewa sai da ya kwashe shekara uku da rabi a cikin mahaifiyarsa kafin a haife shi zuwa duniya
  • Amosun ya bayyana hakan ne a wajen addu'ar tunawa da mahaifiyarsa wacce ta bar duniya shekara 25 da suka gabata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, ya ce mahaifiyarsa ta ɗauke shi a cikinta na tsawon shekara uku da rabi.

Amosun ya ce zuwansa duniya abin al’ajabi ne domin mutane da yawa ba su yarda cewa shi mutum ba ne a lokacin haihuwarsa, saboda ya daɗe a ciki kafin a haife shi.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya fadi babban kalubalen shugabannin Arewa

Amosun ya shafe shekaru a cikin mahaifiyarsa
Ibikunle Amosun ya yi shekara uku da rabi a cikin mahaifiyarsa Hoto: Senator Ibikunle Amosun
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen addu’ar tunawa da mahaifiyarsa Rafatu Sanusi-Amosun karo na 25 da aka gudanar a gidan iyalan Amosun da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ibikunle Amosun ya ba da labarin haihuwarsa

Mahaifiyar tsohon gwamnan ta rasu ne a ranar 27 ga watan Oktoban 1999.

A wajen taron, Ibikunle Amosun ya jaddada muhimmancin girmama iyaye ko da bayan rasuwarsu.

"Na yi shekara uku da rabi a cikin mahaifiyata. Mahaifina wanda ba ya nan a lokacin, har ya shirya a sayo man fetur a ƙona jikina idan ban zo da rai ba."
"Lokacin da aka haife ni, mutane da yawa sun gudu, sun kasa yarda cewa ni mutum ne, amma ga ni a yau, da rai da lafiya."

- Ibikunle Amosun

Amosun ya bayyana cewa wannan na daga cikin dalilin da ya sa mahaifinsa ya sanya masa sunan 'Duro-o-rike' wanda hakan ke nufin 'Ka rayu ka samu kulawar da ta dace'.

Kara karanta wannan

Minista ya yi wata magana, ya roki ƴan Najeriya su ci gaba da yi wa Tinubu addu'a

Yayan tsohon gwamnan, Abidoye Amosun, ya tabbatar da labarin, inda ya ƙara da cewa kwanaki uku kafin bikin suna, mahaifinsu ya aiko da wasiƙa mai ɗauke da sunan da za a sanyawa jaririn.

Tsohon gwamna ya fallasa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun yace Gwamna mai-ci, Dapo Abiodun ya lashe zabe a 2019 ne ta hanyar magudi da murdiya.

Sanata Ibikunle Amosun ya bayyana wannan ne a lokacin da aka ba shi lambar yabo a wajen taron da kungiyar Abeokuta Club ta shirya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng