2019: Gwamna Amosun ya ba mutane hakuri su zabi Shugaba Buhari

2019: Gwamna Amosun ya ba mutane hakuri su zabi Shugaba Buhari

- Ibikunle Amosun yayi magana game da rikicin siyasar Jihar Ogun

- Gwamnan yace babu hannun Buhari a cikin shirin da APC ta ke yi

- Amosun yace babu wanda ya isa ya murde zaben da za ayi a Ogun

- Jam'iyyar APC ta ba wanda ba su tare da Gwamna mai-ci tuta a Jihar

2019: Gwamna Amosun ya ba mutane hakuri su zabi Shugaba Buhari
Ana rikici tsakanin APC da Amosun kan 'Dan takarar Gwamna
Asali: Depositphotos

Mun samu labari cewa gwamna Ibikunle Amosun yayi magana game da abin da ya faru a jihar a farkon makon nan lokacin da jam’iyyar APC ta zo yawon yakin neman zabe a jihar inda taron ya koma wajen rikicin siyasa.

Gwamna Amosun yayi magana jim kadan bayan wannan abin takaici ya faru jiya inda ya bayyana cewa yana cigaba da rokon jama’an jihar sa su nuna goyon bayan su ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben da za ayi.

KU KARANTA: An sheka da wasu zuwa asibiti wajen rikicin APC da PDP a Ekiti

Ibikunle Amosun yake cewa babu sa-hannun shugaban kasar a cikin rikicin jihar. Amosun ya nemi mutanen na sa su ba shugaba Buhari goyon baya a zaben da za a gudanar a makon nan a karawar da zai yi da su Atiku Abubakar.

Gidan jaridar Channels TV ta fitar da bidiyon da aka ji Ibikunle Amosun yana rokon jama’a su goyi bayan Buhari. Gwamnan ya zargi wasu manyan APC da kokarin ganin sun kakabawa mutanen Ogun wanda ba su so a zaben bana.

Amosun wanda yake rikici da wasu jiga-jigan APC yace babu ruwan shugaba Buhari da daurawa jama’a wanda jama’a ba su yi na’am da shi ba a karkashin APC, kuma yace duk wani kokarin murde zaben jihar ba zai kai ko ina ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel