A Ƙarshe, Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Dalilin Gaza Kama Yahaya Bello
- Yan Najeriya suna cigaba da sukan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan gaza mika Yahaya Bello ga hukumar EFCC
- Sai dai hadimin Bola Tinubu, Bayo Onanuga ya yi bayani kan dalilin da yasa yan sanda ba su kama Yahaya Bello ba
- A yanzu haka hukumar EFCC na cigaba da neman Yahaya Bello kan wasu makudan kudi da aka zarge shi da karkatarwa a jihar Kogi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta wanke kanta kan rashi taimakawa EFCC ta kama Yahaya Bello.
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa tana bin doka da oda ne a kan kokarin kama Yahaya Bello da EFCC ke yi.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya yi bayani a wata hira da Channels Television ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin gaza kama Yahaya Bello
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce Yahaya Bello na buya a cikin rigar kariyar gwamnan Kogi.
Bayo Onanuga ya ce gwamna Usman Ododo yana da rigar kariya kuma duk wanda ya fake a karkashinsa ba za a iya kama shi ba.
Onanuga ya bayyana cewa lamarin ba a kan Yahaya Bello ya fara faruwa a duniya ba.
Ga abin da ya ce:
"Jami'an DSS da yan sanda ba za a su iya komai ba wajen kama Yahaya Bello idan ya buya a gidan gwamna Usman Ododo.
Gwamna Usman Ododo yana da rigar kariya, idan aka kama wanda ya fake a karkashinsa an karya doka.
A karkashin haka, yan sanda da DSS ba za su iya taimakawa EFCC ba a kan lamarin."
-Bayo Onanuga
Hukumar EFCC na cigaba da neman Yahaya Bello ido rufe kuma ita ma ta zargi gwamnan Kogi da ba shi kariya.
Jigawa ta fita daga shari'a da EFCC
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da ficewarta daga ƙarar da ke neman a soke hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC).
Rahotanni na nuni da cewa kwamishinan shari'a na jihar Jigawa ne ya sanar da janyewar a ranar Asabar, 26 ga watan Oktoban 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng