Dubu Ta Cika: 'Yan Sanda Sun Cafke Kansila kan Yunkurin Garkuwa da Mutane
- Rundunar ƴan sandan jihar Delta ta yi nasarar cafke wani tsohon kansila bisa zarginsa da yunƙurin yin garkuwa da mutane
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Bright Edafe, ya sanar da cafke tsohon kansilan a cikin wata sanarwa da ya fitar
- Bright Edafe ya bayyana cewa an cafke tsohon kansilan ne bayan an samu sahihan bayanai kan shirin da yake kitsawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Delta - Rundunar ƴan sandan jihar Delta ta sanar da cafke wani tsohon kansila bisa zarginsa da hannu a yunƙurin yin garkuwa da mutane.
Ƴan sandan sun ce an cafke tsohon kansilan mai suna Mista Okechhukwu, bisa zarginsa da hannu a yunƙurin sace wata mata a ƙauyen Abbi a ƙaramar Ndokwa ta Yamma.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, Mista Bright Edafe, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan sanda sun cafke tsohon kansila
Kakakin ƴan sandan ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan DPO na Abbi, Florence Onum, ta samu sahihan bayanan sirri kan cewa akwai shirin yin garkuwa da wata babbar mata a Abbi, rahoton Premium Times ya tabbatar.
Bright Edafe, ya ce jami’an ƴan sanda sun fara gudanar da bincike bayan samun bayanan sirrin inda a ranar 21 ga Oktoba, da misalin ƙarfe 9:00 suka cafke kansilan wanda ya fito daga ƙauyen Emu-Uno da wani mutum ɗaya.
"Wanda ake zargin ya bayyana cewa an dakatar da shi daga zama kansila. Ya kuma bayyana cewa yana so ya sace matar ne domin ƙaramar hukumar ta biya kuɗin fansa tunda ya san matar na kusa da ciyaman."
"Wanda ake zargin yana tsare kuma ana ci gaba da gudanar da bincike."
- Bright Edafe
Ƴan sanda sun fafata da masu garkuwa da mutane
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan jihar Plateau sun yi musayar wuta da masu garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu.
Ƴan sandan sun samu nasarar kuɓutar da wani da aka yi garkuwa da shi mai suna John Kwatsen, bayan wani ƙazamin artabu da masu garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu.
Asali: Legit.ng