'Kamar Lokacin Buhari,' Lauya Ya Tono Kuskuren Tinubu kan Naɗa Ministoci
- Wani lauya masanin tsarin mulkin kasa ya bayyana kuskuren da aka samu wajen zaben sababbin ministoci da shugaba Bola Tinubu ya yi
- Farfesa Mike Ozekhome ya ce Bola Tinubu ya bi tafarkin shugaba Muhammadu Buhari wajen karya dokar kasa yayin nada ministoci
- A daya ɓangaren, lauyan ya bayyana wani kokari da shugaba Bola Tinubu ya yi a Najeriya yayin sauye sauye da ya yi a makon da ya wuce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Masana doka sun fara sharhi kan yadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada wasu ministoci a makon da ya wuce.
Lauya kuma masanin doka, Farfesa Mike Ozekhome ya ce akwai kuskure da Bola Tinubu ya yi wajen nada ministoci.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Farfesa Mike Ozekhome yana cewa Tinubu ya bi hanyar Muhammadu Buhari wajen karya doka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kuskuren Tinubu wajen nada ministoci
Babban lauya masanin tsarin mulkin Najeriya, Farfesa Mike Ozekhome (SAN) ya ce Bola Tinubu bai bi doka ba wajen nada sababbin ministoci.
Farfesa Mike Ozekhome ya bayyana cewa matakin da Tinubu ya bi wajen daukar ministoci ya saba kundin Najeriya na 1999.
"Idan aka lura za a ga cewa sababbin ministoci uku sun fito ne daga jihar Ogun wanda daga can ministan kudi, Wale Edun ya fito.
Ya za a yi a ce karamar jiha kamar Ogun ta samu ministoci hudu a kasa mai jihohi 34, ta ina sauran jihohi za su samu wakilci?
Nada ministocin ya saba dokar Najeriya, kuma canje canjen da aka yi ma ba wata fa'ida zai yi ba."
-Farfesa Mike Ozekhome, Lauya
Farfesa Ozekhome ya fadi kokarin Tinubu
A daya bangaren, Farfesa Mike Ozekhome ya ce Bola Tinubu ya yi kokari wajen hada ma'aikatun cigaban yankunan Najeriya a waje daya.
The Guardian ta wallafa cewa lauyan ya ce hada ma'aikatar cigaban Neja Delta da wasu yankunan Najeriya abu ne mai kyau da zai taimaka sosai.
Kungiyar Arewa ta soki Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sha suka daga wata kungiyar Arewacin Najeriya kan umarnin da ya ba ministoci.
A ranar Alhamis da shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci ministoci da manyan jami'an gwamnati da su rage ayari da jami'an tsaro.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng