An Kama Mai Gadi Ya Ciro Kawunan Mutane a Maƙabarta

An Kama Mai Gadi Ya Ciro Kawunan Mutane a Maƙabarta

  • Rahotanni da suka fito daga jihar Legas na nuni da cewa an kama wani mai gadin maƙabarta da ake zargi ya haɗa kai da wasu miyagun mutane
  • Ana zargin cewa mai gadin maƙabartar na hada kai da wasu mutane wajen sace sassan jikin wadanda suka mutu aka birne su
  • Rundunar yan sanda ta tabbatar da kama mai gadin da wasu mutane kuma ta yi karin haske kan kokarin kama sauran miyagun da suka tsere

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Rundunar yan sanda ta tabbatar da kama wani mai gadin maƙabarta da wasu mutane biyu da kawunan mutane.

Ana zargin cewa mai gadin maƙabartar na hada baki da wasu mutane wajen sace sassan jikin gawa.

Kara karanta wannan

An bi gida gida, an kashe mutane a rikicin manoma da makiyaya

Lagos
An kama mai gadin makabarta a Legas. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a wata maƙabarta a yankin Murikaza a karamar hukumar Agege.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai gadi ya cire kawunan mutane

The Guardian ta wallafa cewa an kama wani mai gadin maƙabarta da wasu mutane ɗauke da kawunan mutane 5 a wata maƙabarta a jihar Legas.

Yan banga a yankin Murikaza ne suka kama mutanen da ake zargin kuma sun mika su ga jami'an tsaro. Ga abin da shaidar gani da ido ya ce:

"Yan banga sun ga mai gadin maƙabarta ya daura wani buhu a kan katanga da ba su yarda da shi ba.
Da aka bukaci ya bude buhun domin bincike sai ya ce ai ganye ya tara domin amfanin gida amma da aka matsa masa sai ya bude shi.
Yana bude buhun kuma sai aka ga kawunan mutane ne guda biyar, kuma dama an taba kama shi da sassan dan Adam."

Kara karanta wannan

Tirelar Dangote ta markaɗa ɗan acaɓa har lahira yayin da suka yi karo

- Isiaka Amosu, shaidar gani da ido

Bayanin yan sanda a jihar Legas

Rundunar yan sanda a Isokoko ta bayyana cewa mutane uku suna hannunta kuma ana ƙoƙarin cafko wadanda suka gudu.

Wani dan sanda ya bayyana cewa za a mika lamarin wadanda ake zargin zuwa sashen binciken masu manyan laifuffuka.

An kama mai sata a makabarta

A wani rahoton, kun ji cewa al'ummar Falasɗinawa na cigaba da shiga tashin hankali mai muni yayin da yakin da suke yi da Isra'ila ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

An ruwaito cewa an samu kashe kashe da dama a baya bayan nan wanda har aka samu ƙarancin wuraren da za a birne gawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng