Gidajen Mai Wayam, Yan Najeriya Sun Fara Hakura da Amfani da Fetur
Bayan kokawa da jama'ar kasar nan su ka yi kan karin farashin litar fetur zuwa sama da ₦1,000, sun fara daukar mataki tun da gwamnati ta yi biris da su.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
An gano cewa jama'ar kasar nan sun fara kauracewa gidajen mai, inda ake ganin wasu daga gidajen wayam babu masu sayen fetur.
Daily Trust ta tattaro cewa masu ababen hawa a jihohin Kano, Kaduna, Gombe, Borno, Kwara, da Legas sun fara hakura da amfani da abin hawansu saboda tsadar fetur.
1. Kano: Jama'a sun fara ajiye ababen hawansu
Ma'aikata da dama a jihar Kano sun fara ajiye motoci da baburansu saboda tsadar da fetur ya yi, inda wasu su ka rungumi amfani da Keke Napep.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu kuma da wuraren aikinsu ba nisa daga gidajensu sun koma tafiyar kafa zuwa wajen aiki.
Tijjani Muhammad, ma'aikaci ne a asibitin Malam Aminu Kano (AKTH), ya bayyana cewa tuni ya ajiye motarsa a gida.
Ya kara da cewa hatta yaransa, yanzu ya daina kai su makaranta sai dai su hau motocin haya ko su taka da kafarsu.
2. Jama'a sun rage sayen fetur a Kaduna
Wani manaja a gidan mai da ke Kaduna, Alhaji Balarabe Salis ce masu sayen fetur sun ragu da kusan 50% saboda tsadar da ya yi.
Ya bayyana cewa kafin karin farashin fetur, su kan sayar da akalla lita 5,000 ta fetur a rana, amma yanzu da kyar su ke sayar da lita 2,000 a kullum.
Alhaji Tajudeen Ajigbade, wani mazaunin jihar Kaduna ne, ya kuma bayyana cewa ba ya hawan abin hawansa sai da dalili mai muhimmancin gaske.
3. Iyaye sun rage shan fetur a Borno
Wasu iyaye a jihar Borno sun bayyana cewa karin farashin fetur ya sa sun rage zirga-zirga da yaransu zuwa makaranta a motocinsu.
Wani mazaunin Bulumkutu a Borno ya bayyana cewa yanzu idan ya kai yaransa makaranta, sai ya ajiye motarsa a kusa da makarantar yaran, ya hau motar haya zuwa wajen aiki.
Ya kara da cewa da an tashi daga makaranta sai ya dawo ya dauke su a motar, kuma wannan dabara ta na taimakonsa wajen rage shan mai sosai.
4. Kwara: An samu raguwar sayar da fetur
Wani manajan gidan fetur da ke Offa Garage a jihar Kwara da ya nemi a sakaye sunansa ya ce an samu raguwar sayar da fetur da 25%.
Ya bayyana cewa kafin yanzu, su kan sayar da litar fetur 11,000, amma yanzu da kayar ake sayar da lita 8,000.
Manajan ya ce da zarar an yi wa fetur kishiya, jama'a za su rage amfani da shi da akalla 50%.
5. Gidajen man Legas sun rage sayar da fetur
Bincike ya nuna cewa wasu gidajen mai sun daina sayar da fetur a jihar Legas, yayin da wasu su ka rage sayar da man.
Daya daga cikin gidajen mai da ke Ikeja a Legas ya bayyana damuwa kan yadda ake cigaba da samun raguwar sayen man fetur.
Guda daga cikin manajojin gidan man NNPCL ya bayyana cewa duk wanda ya cika tankin motarsa, ba ya dawowa sai karshen wata.
Tinubu ya kawo kishiyar man fetur
A wani labarin kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce jama'a za su iya sayen iskar gas samfurin CNG a kan ₦200 kowace lita a maimakon fetur da ya haura ₦1,000.
Karamin ministan albarkatun mai (gas), Ekperipke Ekpo ya bayyana cewa shugaban kasa Tinubu na son a mayar da gidajen mai wurin sayar da gas din CNG don saukakawa yan kasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng