Miyagun Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Babban Malami a Najeriya

Miyagun Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Babban Malami a Najeriya

  • Ƴan bindiga sun yi awon gaba da wani malamin coci a Awkuzu da ke ƙaramar hukumar Oyi ta jihar Anambra a shiyyar Kudu maso Gabas
  • Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar sun yi awon gaba da faston a ƙofar shiga cocin ranar Asabar da ta gabata
  • Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sanda a jihar Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya bayyana cewa har yanzu ba su samu rahoton kai harin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Anambra - Wasu miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da babban malamin cocin St. James’ Parish da ke garin Awkuzu jiha Anambra, Venerable David Ajaefobi.

Rahotannin da muka samu sun nuna cewa ƴan bindigar sun yi awon gaba da limamin cocin ne a kofar shiga St. James’ Parish a Awkuzu ranar Asabar da ta wuce.

Kara karanta wannan

Kaico: Ɗalibai 2 sun mutu a wani harin kwantan ɓauna, mutane sun shiga jimami

Taswirar jihar Anambra.
Yan bindiga sun yi awon gaba da limamin coci a jihar Anambra Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Shin ƴan bindigar sun nemi kudin fansa?

Har zuwa loƙacin da aka tattara wannan rahoton maharan ba su tuntuɓi kowa daga cikin dangin Ajaefobi ba, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar wasu rahotanni, ƴan bindigar ba su kira iyalan limamin cocin ko suka nemi kuɗin fansa ba, sannan har yanzu ba a san dalilin garkuwa da shi ba.

Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?

Zuwa yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ƴan sanda reshen jihar Anambra kan wannan sabon harin.

Da aka nemi jin ta bakinsa, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan, SP Tochukwu Ikenga, ya ce ba a kawo masu rahoton kai harin ba.

A halin da ake ciki yanzu rahotanni sun nuna cocin ta fara gudanar da addu’o’i domin wanda aka yi garkuwa da shi ya kubuta cikin ƙoshin lafiya.

Kara karanta wannan

Tsohuwar Minista ta taimaka wajen samo $57.5bn domin kafa Biafara? Gaskiya ta fito

Ƴan bindiga sun kai hari kusa da jami'a

A wani rahoton na daban yan bindiga da ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne sun kai hari a kusa da jami'ar Nnamdi Azikiwe (UNIZIK) da ke jihar Anambra

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa an kashe aƙalla mutane shida a harin na safiyar ranar Alhamis, 24 ga watan Oktoban 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262