"Yana Cikin Hadari": Shugaban Majalisa Ya Fadi Abin da Kashim Shettima Ke Bukata

"Yana Cikin Hadari": Shugaban Majalisa Ya Fadi Abin da Kashim Shettima Ke Bukata

  • Shugaban majalisar dokokin jihar Borno, Abdulkarim Lawan ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta sayo sabon jirgin sama ga Kashim Shettima
  • Abdulkarim Lawan ya bayyana cewa rayuwar mataimakin shugaban ƙasan na cikin haɗari saboda jirgin saman da yake amfani da shi
  • Kalamansa na zuwa ne bayan jirgin Kashim Shettima ya samu wata matsala a filin jirgin sama na JFK da ke birnin New York

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Shugaban majalisar dokokin jihar Borno, Abdulkarim Lawan, ya ce rayuwar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima na cikin haɗari.

Shugaban majalisar ya ce rayuwar Shettima na cikin haɗari ne sakamakon lalataccen jirgin shugaban ƙasa da yake amfani da shi wajen wakiltar Shugaba Bola Tinubu a wajen taruka a faɗin duniya.

Kara karanta wannan

'Wani abu ya samu jirginsa,' Shettima ya fasa zuwa taron da Tinubu ya turasa wakilci

An bukaci a sayowa Kashim Shettima jirgin sama
An bukaci a sayowa Kashim Shettima sabon jirgin sama Hoto: @StanleyNkwocha
Asali: Twitter

Jirgin saman Shettima ya samu matsala

Jaridar Daily Trust ta ce yea faɗi haka ne bayan Shettima ya soke tafiyarsa zuwa taron CHOGM da aka yi a Samoa saboda wani abu da ya faru a filin jirgin saman birnin New York na Amurka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar fadar shugaban ƙasa, Shettima ya fasa zuwa Samoa ne saboda wani abu da ya bugi jirginsa a lokacin da ya tsaya a filin jirgin sama na JFK da ke birnin New York.

An buƙaci a sayo sabon jirgi ga Shettima

Da yake tsokaci kan lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar Lahadi, Lawan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sayowa Shettima sabon jirgin sama domin kaucewa aukuwar abin da ba a so.

Ya ce jirgin da aka ba mataimakin shugaban ƙasan ya sha fama da matsaloli da dama a ƴan kwanakin nan, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya tura sako ga Tinubu awanni bayan raba shi da mukaminsa

Ya yi godiya ga Allah saboda kare rayuwar Shettima da sauran mutanen da ke tattare da shi yayin da ya yi kira ga gwamnatin tarayya kan ta gudanar da bincike kan lamarin.

"Rayuwar mataimakin shugaban ƙasa da ta ƴan tawagarsa suna cikin haɗari yayin amfani da tsohon jirgin shugaban ƙasa mara kyau."
"Don haka akwai bukatar a sayo sabon jirgin sama ga Sanata Kashim Shettima domin gujewa sake faruwar irin waɗannan matsalolin."

- Abdulkarim Lawan

Tinubu ya tura Shettima wani taro

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya wakilce shi a wajen taron CHOGM.

Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa wajen taron shugabannin ƙasashe rainon Ingila (CHOGM) na shekarar 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng