Lalacewar Wuta: Atiku Ya Dauki Zafi kan Lamarin, Ya Kawo Hanyar Dakile Matsalar

Lalacewar Wuta: Atiku Ya Dauki Zafi kan Lamarin, Ya Kawo Hanyar Dakile Matsalar

  • Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da rashin wutar lantarki musamman a Arewacin Najeriya
  • Atiku ya ce abin takaici ne har yanzu ƙasar na fama da matsalolin wutar lantarki da yawan lalacewarta duk bayan wani lokaci
  • Hakan ya biyo bayan rasa wutar lantarki a wasu yankunan kasar da dama da kuma Arewacin Najeriya baki daya a yan kwanakin nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi magana kan lalacewar wuta a Arewacin Najeriya.

Atiku ya ce abin takaici ne har yanzu Najeriya na fama da matsalar wutar lantarki da yawan lalacewarta.

Kara karanta wannan

'Abin takaici ne': Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan kiran juyin mulki, ta yi gargadi

Atiku ya yi Allah wadai da yawan lalacewar wutar lantarki
Atiku Abubakar ya koka kan rashin wuta, ya bada shawarar yadda za a dakile matsalolin. Hoto: Atiku Abubakar.
Asali: Getty Images

Atiku ya koka da yawan daukewar wuta

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya fadi haka ne a daren jiya Asabar 26 ga watan Oktoban 2024 a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya yi Allah wadai da yawan daukewar lantarki musamman a yankunan Arewacin Najeriya.

Ya shawarci ma'aikatu da hukumomi da ke da alhakin gyaran wurar da su yi gaggawar daukar mataki domin shawo kan matsalar.

"Duba da yanayin rashin wuta a yankin Kudu maso Gabas da Arewacin Najeriya gaba daya, ya kamata hukumomi su yi gaggawar shawo kan lamarin."
"Na yi imani a tsare-tsare na, akwai tsarin kawo karshen rashe-rashen wuta da ake fama da shi a Najeriya baki daya."

- Atiku Abubakar

Lalacewar wuta: Atiku ya nemo mafita ga Najeriya

Atiku ya kuma ba da shawarar ba jihohin damar samar da wutar lantarki ga al'ummarsu domin dauke ikon daga Gwamnatin Tarayya.

Kara karanta wannan

Matsalar lantarki: TCN ya fadawa yan Arewa gaskiya kan halin da za a shiga

Ya kuma bukaci ma'aikatu da kamfanoni masu zaman kansu su zuba hannun jari a kamfanin wuta domin inganta ɓangaren.

Lalacewar wuta: Kamfanin TCN ya yi magana

Kun ji cewa Kamfanin rarraba lantarki na kasa (TCN) ya yi magana kan yadda wuta za ta cigaba da kasancewa a Arewa.

TCN ya ce akwai yiwuwar cigaba da samun matsalar wutar lantarki a Arewacin Najeriya saboda wasu dalilai masu karfi.

Hakan ya biyo bayan lalacewar wutar lantarki musamman a Arewacin Najeriya da aka shafe kwanaki ana fama da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.