Ana cikin Halin Kunci, Tinubu Ya Ware Gwamna 1 a Najeriya, Ya Yaba Masa

Ana cikin Halin Kunci, Tinubu Ya Ware Gwamna 1 a Najeriya, Ya Yaba Masa

  • Ana cikin halin kunci a Najeriya, Shugaba Bola Tinubu ya yabawa Gwamna daya a Najeriya kan irin kokarin da yake yi
  • Tinubu ya yabawa gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji kan kokarin kawo sauyi da yake yi a jihar domin inganta ta
  • Shugaban wanda ya samu wakilcin Sanata Opeyemi Bamidele ya wakilta ya ce zai ci gaba da ba shi gudunmawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yabawa gwamnan Ekiti kan ayyukan raya kasa da yake yi.

Tinubu ya kira sunan Gwamna Biodun Oyebanji na musamman inda ya fadi alherin da yake yiwa al'umma.

Kara karanta wannan

'Abin takaici ne': Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan kiran juyin mulki, ta yi gargadi

Tinubu ya yabawa Gwamna 1 a Najeriya
Bola Tinubu ya yabawa Gwamna Biodun Oyebanji kan ayyukan alheri da yake yi. Hoto: Biodun Oyebanji, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Tinubu ya sha alwashin tallafawa gwamnan Ekiti

Shugaban kasar ya bayyana haka ne yayin bikin cika shekaru biyu na gwamnan a birnin Ado-Ekiti, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya yi alkawarin tsayawa kafada da kafada da shi domin inganta al'ummar jihar Ekiti, Vanguard ta ruwaito.

Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele shi ya wakilci Tinubu a taron da aka gudanar.

Tinubu ya yabawa gwamna musamman kan aikin alheri

"Ba zan so tsayawa a nan ba, na ce shugaban kasa yana sonka, ka sani yana sonka kuma yana baka dukan goyon baya."
"Na sha wayar da kan mutane da ke cece-kuce kan gadar sama da kake ginawa, na ce musu kana samun tallafi ne daga Gwamnatin Tarayya."
"Tabbas kana iya bakin kokari wurin tsamo jihar daga cikin kangi da kuma kawo sauyi a cigaban jihar."

Kara karanta wannan

Minista ya yi wata magana, ya roki ƴan Najeriya su ci gaba da yi wa Tinubu addu'a

- Bola Ahmed Tinubu

Tinubu ya yi gargadi kan kiran juyin mulki

Kun ji cewa Gwamnatin Bola Tinubu ta yi magana kan kiraye-kirayen juyin mulki da ake yi a Najeriya musamman a wannan yanayi da ake ciki.

Gwamnatin ta yi Allah wadai da yada rahotanni da ke neman ta da tarzoma a fadin Najeriya baki daya wurin kiran yan Najeriya kan juyin mulki.

Hakan ya biyo bayan wani rahoto da jaridar The Guardian ta wallafa da gwamnatin ke ganin ya saɓa aikin jarida da kuma neman ta da rigima a ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.