'Yan Sanda Sun Yi Musayar Wuta da Masu Garkuwa da Mutane
- Jami'an rundunar ƴan sandan jijar Plateau sun yi artabu da wasu masu garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu
- Ƴan sandan bayan fafatawa da masu garkuwa da mutanen sun samu nasarar kuɓutar da wani matashi da suka sace
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Plateau ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 26 ga watan Oktoban 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Plateau sun yi musayar wuta da masu garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu.
Ƴan sandan sun samu nasarar kuɓutar da wani da aka yi garkuwa da shi mai suna John Kwatsen, bayan wani ƙazamin artabu da masu garkuwa da mutane a wani daji da ke yankin Rantiya a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu.
Ƴan sanda sun fafata da masu garkuwa da mutane
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Plateau, Alabo Alfred ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Jos ranar Asabar, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa wasu ƴan bindiga ne suka sace matashin mai shekaru 38 da ke zaune a Port Harcourt a cikin motarsa lokacin da ya ziyarci Jos, babban birnin jihar.
Ya ce an sanar da jami’an ƴan sanda na Rantiya faruwar lamarin na sace matashin.
Alabo Alfred ya ce bayan samun rahoton sun jagoranci sauran jami’ai zuwa wani tsauni da ke yankin tare da yin artabu da masu garkuwa da mutanen, kuma daga bisani suka ceto mutumin da aka sace.
Ƴan sanda sun cafke dattijuwa
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Yobe ta ce ta kama wata Hamsatu Modu mai shekaru 54 dauke da harsasan bindiga 350.
Rahotanni sun bayyana cewa ƴan sanda sun cafke dattijuwar ne a kauyen Morami da ke karamar hukumar Jakana Konduga ta jihar Borno.
Ana dai zargin Hamsatu Modu ta dauko alburusan ne daga garin Buni Yadi domin kaiwa ƴan bindiga a jihar Yobe.
Asali: Legit.ng