Gwamnan PDP ya ba Ma'aikata Mamaki, Zai ba su Albashin N80,000, an Fadi Lokacin Biya

Gwamnan PDP ya ba Ma'aikata Mamaki, Zai ba su Albashin N80,000, an Fadi Lokacin Biya

  • Yayin da ake cigaba da amincewa da sabon albashi a jihohi, Gwamnan Bayelsa ya fadi yadda zai biya
  • Gwamna Diri Douye ya amince da biyan N80,000 a matsayin sabon albashi ga ma'aikatan jihar
  • Amincewa da N80,000 ya sanya gwamnan zama na shida a cikin gwamnoni da suka amince da albashi mai tsoka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bayelsa - Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya yi albishir ga ma'aikatan jihar da sabon albashi.

Diri ya amince da biyan N80,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar.

Gwamnan PDP ya amince da biyan ma'aikata N80,000
Gwamna Douye Diri ya amince da biyan N80,000 ga ma'aikatan jihar Bayelsa. Hoto: @govdouyediri.
Asali: Twitter

Gwamnan ya tabbatar da haka ne a jiya Asabar 26 ga watan Oktoban 2024 a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: Gwamna ya amince da biyan N70,000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Diri ya sanar da sabon albashin ga ma'aikata wanda ya yi daidai da na gwamnoni uku a Najeriya.

Gwamnonin da za su biya N80,000 zuwa sama

Gwamnonin sun hada da Umar Bago na Niger da Umo Eno na Akwa Ibom sai kuma Peter Mbah na jihar Enugu.

Sai dai gwamnoni gida biyu sun yi fice inda suka amince da biyan N85,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Gwamnonin guda biyu da suka fi kowa su ne Babajide Sanwo-Olu na Lagos da Siminalayi Fubara daga jihar Rivers.

Gwamnan PDP zai biya ma'aikata N80,000

Gwamna Diri na Bayelsa ya ce ma'aikata sun cancanci biyan albashi mai tsoka duba da halin kunci da ake ciki.

Sanarwar ta ce gwamnatin jihar za ta fara biyan albashin ne a watan Nuwambar 2024 da muke ciki.

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: Gwamna ya fara hasashen biyan N1m ga ma'aikata

"Na sanar da biyan N80,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata."
"Ma'aikata sun cancanci karbar kuɗi mai tsoka idan aka yi duba zuwa ga halin da kasa ke ciki a yanzu."
"Sabon mafi ƙarancin albashin zai fara aiki ne a ranar 1 ga watan Nuwambar 2024, nagode da hakuri da kuke nunawa."

- Douye Diri

Gwamna Inuwa zai biya mafi ƙarancin albashi

Kun ji cewa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da biyan sabon mafi ƙarancin albashi a jihar Gombe.

Gwamna Inuwa ya tabbatar da haka ne makwanni kadan bayan ya ce jihar ba za ta iya biyan albashin N70,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.