'Abin Takaici ne': Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana kan Kiran Juyin Mulki, Ta Yi Gargadi
- Fadar shugaban kasa ta yi Allah wadai da kiraye-kirayen da ake yi a Najeriya kan neman a yi juyin mulkin soja
- Fadar ta yi wannan magana ne a cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta ce abin takaici ne yadda ake mantawa da alherin gwamnatin
- Hakan ya biyo bayan wani rahoto da wata jarida ta buga kan halin kunci da ake ciki da bai yiwa gwamnatin dadi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Fadar shugaban kasar Najeriya ta yi martani kan kiraye-kiraye juyin mulki a kasar.
Fadar ta yi Allah wadai kan wani rahoto da wata jarida ta wallafa da ke neman kawo rigima a kasa.
Gwamnatin Tinubu ta soki masu neman rigima
Hadimin Bola Ahmed Tinubu a bangaren sadarwa, Bayo Onanuga shi ya bayyana haka a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce bai kamata ana amfani da irin kalaman tunzura al'umma ba wurin fakewa da aikin jarida.
Onanuga ya ce bayanin da ke kunshe a labarin ta da tarzomar da aka yi ya saba ka'idar aikin jarida a Najeriya.
Ya zargi gidajen jaridu da kushe gwamnatin Bola Tinubu yayin da take mantawa da abubuwan alheri da take yi.
"Tsarin mulkin soja ya saba cigaban al'umma da wayewar dimukraɗiyya duk yadda aka yi masa gyaran fuska."
"Amma duk da haka ana kiran tunzura al'umma kan gwamnatin Bola Tinubu da cewa bai tausayawa al'umma fiye da mulkin soja."
"Wadannan kiraye-kirayen sun yi fatali da wahalar da aka sha wurin kwato yancin dimukraɗiyya a kasa."
- Fadar shugaban kasa
Dalilin ba da hakuri da Tinubu ke yi
Sanarwar ta ce Bola Tinubu yana cigaba da kiran al'umma da su kara hakuri kan halin kunci da ake ciki.
Ta ce kiran a kara hakuri da Tinubu ke yi ba wai gajiyawa ba ne wurin kawo sauyi a kasar domin saukakawa al'umma.
Wike ya roki addu'a ga Bola Tinubu
Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya sake rokon al'umma kan taya mai girma shugaban kasa, Bola Tinubu addu'a.
Wike ya ce hakan ne kadai zai taimaka wurin shawo kan matsalolin kasar kamar yadda Tinubu ke kokarin dakilewa.
Asali: Legit.ng