Sifetan Dan Sanda Ya Bindige Fitaccen Mawaki a Najeriya, Rundunar Ta Dauki Mataki

Sifetan Dan Sanda Ya Bindige Fitaccen Mawaki a Najeriya, Rundunar Ta Dauki Mataki

  • Rundunar yan sanda da tsare wani sifetanta kan zargin hallaka wani fitaccen mawaki a jihar Enugu da ke Kudancin Najeriya
  • Rundunar ta tabbatar da kama dan sandan inda ta ce an fara kaddamar da bincike kan zarginsa da kisan kai
  • Mawakin mai suna Okezie Mba da aka fi sani da Igbo-Jah ya rasa ransa bayan harsashen dan sanda ya fasa shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Enugu - Wani jami'in rundunar yan sanda a jihar Enugu ya bindige wani fitaccen mawaki har lahira.

Marigayin Okezie Mba ya rasa ransa ne a hannun wani sifetan dan sanda a Enugu da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan kacaniyar Seamnan Abbas, sojoji sun sake tsare sojan ruwa, an gano dalili

Wani dan sanda ya bindige mawaki har lahira
Sifetan dan sanda ya bindige wani matashin mawaki a jihar Enugu. Legit.
Asali: Original

Dan sanda ya bindige mawaki a Enugu

Premium Times ta tabbatar da cewa Mbah ya je ofishin yaki da kungiyoyin asiri ne lokacin da jami'an tsaro suka fara harbe-harbe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya ta ce an wuce da marigayin da aka fi sani da Igbo-Jah zuwa asibiti inda ya ce ga garinku.

"Harsashi ya samu Igbo-Jah, sun yi kokarin kai shi asibiti amma ya rasa ransa yayin da ake kan hanya."

- Cewar majiyar

Yadda mawaki ya rasa ransa saboda sakaci

Kakakin rundunar yan sanda a jihar, Daniel Ndukwe ya tabbatar da faduwar lamarin a yau Asabar 26 ga watan Oktoban 2024.

Ndukwe ya ce tuni aka cafke dan sandan da ya bindige mawakin inda ya ce an fara bincike kan lamarin.

"Mawakin yana kokarin barin ofishin yan sanda bayan ziyarar abota inda wani sifeta ya bindige shi wanda har yanzu ba a dalili ba."

Kara karanta wannan

Ana matsalar lantarki. 'yan Arewa sun dura kan Tinubu, sun ragargaje shi

"An kwashi Mbah zuwa asibiti inda likita ya tabbatar da cewa mawakin rasa ransa, an ajiye shi a dakin adana gawarwaki."

- Daniel Ndukwe

Ana zargin basarake da garkuwa da matashi

Kun ji cewa wani basarake a jihar Enugu ya shiga matsala bayan zargin yin garkuwa da matashi saboda filin gado.

Ana zargin Ezineso Oduma, Igwe Daniel Okechukwu Njoku da dauke matashi, Michael Njoku da karbar N2.5m.

Iyalan matashin sun roki gwamnatin jihar Enugu da hukumar tsaro ta DSS ta hukunta basaraken kan boye Michael.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.