Uba Sani Ya Sanar da Tinubu Nasarorin da Ya Samu a Mulkin Kaduna

Uba Sani Ya Sanar da Tinubu Nasarorin da Ya Samu a Mulkin Kaduna

  • Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana cewa ya samu nasarar rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar
  • Uba Sani ya bayyana cewa adadin yaran da ba sa zuwa makaranta ya ragu da kusan 300,000 a cikin watanni shida da suka gabata
  • Gwamnan ya ce an samu wannan nasarar ne sakamakon maida hankalin da ya yi wajen bunƙasa ɓangaren ilmi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa ya rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar.

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa adadin yaran da ba sa zuwa makaranta ya ragu da kusan 300,000 a cikin watanni shida da suka gabata, sakamakon zuba jari mai yawa a fannin ilimi.

Kara karanta wannan

Minista ya yi wata magana, ya roki ƴan Najeriya su ci gaba da yi wa Tinubu addu'a

Uba Sani ya gana da Tinubu
Uba Sani ya ce ya rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta ce ya bayyana hakan ne ga manema labarai jiya bayan ya ziyarci shugaban ƙasa Bola Tinubu a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar rahoton da hukumar ƙididdiga ta jihar ta fitar, an ƙiyasta cewa Kaduna tana da yara 768,739 da ba sa zuwa makaranta a matakin farko na ilimi.

Uba Sani ya samu nasara a fannin ilmi

Gwamna Uba Sani ya bayyana nasarorin da jihar ta samu a fannin ilimi da suka haɗa da gina sababbin makarantun sakandire 62 da ajujuwa 2,340 na firamare tare da ɗaukar malamai, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

"Na sanar da shi cewa a cikin watanni shida da suka gabata mun rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta da kusan 300,000 saboda mun gina makarantun sakandare kusan 62, ajujuwa 2,340 a makarantun firamare, mun ɗauki malamai aiki."

Kara karanta wannan

Uba Sani ya fadi sadaukarwar da ya yi bayan zama gwamna

"Har ila yau, mun samu damar sake ginawa, gyarawa da kuma samar da kayan aiki ga cibiyoyin kula da lafiya a mataki na biyu kusan 12 a jihar Kaduna."
"Muna gina hanyoyi 62 waɗanda adadinsu ya kai kimanin kilomita 700 a fadin jihar Kaduna. Wasu daga cikinsu an kammala kuma an ƙaddamar da su. Wasu ana ci gaba da aiki."

Gwamna Uba Sani

Uba Sani ya rage albashinsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana matakan da ya ɗauka domin tsuke aljihun bakin gwamnati.

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa shi da ƴan majalisar zartaswarsa na kan tsarin karɓar rabin albashi da nufin rage kashe kuɗaɗen gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng