Bayan Kacaniyar Seamnan Abbas, Sojoji Sun Sake Tsare Sojan Ruwa, an Gano Dalili

Bayan Kacaniyar Seamnan Abbas, Sojoji Sun Sake Tsare Sojan Ruwa, an Gano Dalili

  • Bayan cakwakiyar da aka yi game da Seamnan Abba Haruna, rundunar tsaro da sake tsare wani sojan ruwa kan kisan kai
  • Rundunar tsaro ta tabbatar da tsare SL Akila A. kan zargin hallaka wani soja a bakin aiki a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya
  • Daga bisani, bayan tsare shi, an kuma kwace makamansa tare da fara kaddamar da bincike mai tsauri kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Rundunar tsaron Najeriya ta tsare wani sojan ruwa kan hallaka abokin aikinsa a jihar Zamfara.

Rundunar ta tsare sojan mai suna A. Akila da aka tura 'Operation Fansan Yamma' a Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

'Yadda 'yan ta'adda ke samun bindigogi da harsasan gwamnati,' sojoji sun yi bayani

Rundunar tsaro ta tsare sojan ruwa kan zargin kisan kai
Rundunar tsaron Najeriya ta tsare sojan ruwa kan zargin hallaka dan uwansa. Hoto: @DefenceInfoNG.
Asali: Facebook

Sojan ruwa ya hallaka dan uwansa a Zamfara

Daraktan yada labaran rundunar, Manjo-janar Edward Buba shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Edward Buba ya ce lamarin ya faru ne a jihar Zamfara a jiya Juma'a 25 ga watan Oktoban 2024.

Manjo-janar Buba ya ce wanda ake zargin ya hahharbi dan uwan nasa a sassan jikinsa ba tare da kakkautawa ba, The Guardian ta ruwaito.

Yadda sojan ruwa ya bindige dan uwansa

"A ranar 25 ga watan Oktoban 2024 da misalin karfe 03:12 sojan ruwa, SL Akila A. da aka tura 'Operation Fansan Yamma' ya bindige dan uwansa."
"Bayan haka, an tsare shi da kwace makamin da ke hannunsa, yayin da aka ƙaddamar da bincike."

- Manjo-janar Edward Buba

Edward Buba ya ce rundunar tana ta kokarin sanar da iyalan sojan da Akila ya hallaka a bakin aiki cikin lalama domin shawo kan lamarin.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan NNPCL sun mutu da jirgin sama ya yi mummunan hatsari, an rasa rayuka

Sojoji sun sallami Seamnan Abbas daga aiki

Kun ji cewa bayan shekaru shida da ake zargin an tsare wani sojan ruwa, Seaman Abbas Haruna, an samu rahoton yanzu sojan ya shaki iskar 'yanci.

Rahoto ya nuna cewa Seaman Abbas ya fara samun sauki bayan kai shi asibiti, amma kuma rundunar soji ta kore shi daga aiki kan lamarin.

Matar Abbas Haruna. Hussaina Iliya ta nuna matukar godiyarta ga dukkanin wadanda suka taimaka har mijinta ya kubuta daga ukubar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel