Lokacin da aka Samu Mutane 4 da Suka Rike Shugabancin INEC a Watanni 3
Abuja - An yi lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta watau INEC ta rika yawo tsakanin shugabanni dabam-dabam.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Hakan ta faru ne a watan Yuli, aka samu mutane da yawa sun jagoranci ragamar hukumar INEC mai shirya zabe.
An ga canjin ne da wa’adin Farfesa Attahiru Jega ya cika, malamin makarantar ya jagoranci zabukan 2011 da 2015.
Shugabanni 4 a hukumar INEC a watanni 3
Legit ta tuno lokacin da jami’ai hudu (4) suka shugabanci hukumar INEC a 2015.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Attahiru Jega (2010 – Yulin 2015)
VOA ta rahoto lokacin da Goodluck Jonathan ya nada Farfesa Attajiru Jega a 2010.
A watan Yulin 2015 ne wa’adin Attahiru Jega da wasu kwamishinonin zabe ya kare kamar yadda hukumar ta shaida a shafinta.
Sauran kwamishinonin da abin ya shafa sun hada da Col. M.K. Hammanga (retd.), Dr. Ishmael Igbani da Dame Gladys Nwafor.
A cikin wadanda suka tafi tare da Farfesa Jega lokacin akwai Farfesa Lai Olurode, Thelma Amata Iremiren da Dr. Nuru Yakubu.
2. Ahmad Wali (Agustan 2015)
Ambasada Ahmad M. Wali bai dade ba a matsayin shugaban INEC na rikon kwarya, ya yi ‘yan kwanaki ne kurum a ofis a hukumar.
Wali ya mikawa Amina B. Zakari shugabancin hukumar zaben da Mai girma shugaban kasa ya yi amfani da ikonsa, ya nada ta.
An ce abin da ya sa ya bar ofis shi ne shugaban Najeriya ne kurum yake da ikon zaben shugaban hukumar INEC ba Attahiru Jega ba.
3. Aisha B Zakari (Agusta – Oktoba 2015)
Da ya tashi tafiya, an ji Wali ya mika shugabanci ne ga Amina Bala Zakari wanda ta na cikin manyan kwamishinonin INEC a Agusta.
Vanguard ta kawo labari cewa an yi ta korafi a lokacin domin ana zargin Amina Bala Zakari ta na da alaka da Muhammadu Buhari.
Jami’ar ta fito ne daga Jigawa, kuma ta samu digiri daga ABU a 1980. Kafin zuwa INEC, ta taba zama mai ba shugaban kasa shawara.
4. Mahmud Yakubu (Oktoba 2015)
Duk bayan an gama karba-ka-mika, sai shugaban kasa ya sanar da nadin Farfesa Mahmud Yakubu a matsayin shugaban INEC a watan Oktoba.
Kamar Jega, shi ma Yakubu Farfesa ne wanda ya kware a kan ilmin tarihi kuma har ya kafa tarihi a lokacin da ya yi digirinsa a jami’ar UDUS.
Bayan wa’adinsa ya cika, shugaba Buhari ya kara nada shi a karo na biyu. Yakubu ya fara kirga kwanaki, zai bar kujerar zuwa shekarar 2025.
SERAP za ta kai hukumar INEC kotu
Rahoto ya gabata cewa kungiyar SERAP za ta maka hukumar INEC a gaban kotu. SERAP ta ce an tafka rashawa da laifuffukan zabe a 2023.
Kungiyar ta ba INEC wa'adin kwanaki bakwai ta binciki gwamnoni da mataimakansu saboda sabawa ka'idojin zabe a shekarar.
Asali: Legit.ng