Kano: Kotu Ta Yi Hukunci kan Yunkurin Dakatar da Zaben Ciyamomi

Kano: Kotu Ta Yi Hukunci kan Yunkurin Dakatar da Zaben Ciyamomi

  • Wata babbar kotu da ke jihar Kano ta yi hukunci kan yunƙurin da wasu jam'iyyun siyasa ke yi na hana gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi
  • Kotun ta ba hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar (KANSIEC) ikon gudanar da zaɓen wanda za a yi a ranar Asabar, 26 ga watan Oktoban 2024
  • Alƙalin kotun ya kuma yi kira ga jami'an tsaro da su samar da tsaro a yayin gudanar da zaɓen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Babbar kotun Kano ta ba hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC) ikon gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomin da aka shirya gudanarwa ranar Asabar.

Babbar kotun ta soke duk wani yunƙuri da jam’iyyun siyasa ke yi na dakatar da zaɓen ƙananan hukumomin.

Kara karanta wannan

Kotu ta jiƙawa jam'iyyar NNPP aiki awanni kafin zaben ƙananan hukumomi a Ƙano

Kotu ta ba da dama a yi zaben ciyamomi a Kano
Kotu ta ba KANSIEC damar gudanar da zabe a Kano Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Kotu ta ba KANSIEC damar yin zaɓe

Alƙalin kotun mai shari’a Sanusi Ma’aji, ya yanke hukuncin cewa KANSIEC tana da ikon gudanar da zaɓe a ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar KANSIEC ce ta kai ƙarar jam’iyyar APC da wasu jam’iyyun siyasa 13.

A hukuncin da ya yanke, mai shari’a Ma’aji ya jaddada cewa duk wani yunƙuri na kawo cikas ga zaɓen bai inganta ba.

"Hukumar KANSIEC, a ƙarƙashin tanade-tanaden kundin tsarin mulki, tana da ikon gudanar da zaɓe a jiha. Duk wani yunƙuri na kawo cikas bai inganta ba."

- Mai shari'a Sanusi Ma'aji

An warware hukuncin soke zaɓe

Alƙalin ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su tabbatar da kare rayuka da dukiyoyi a lokacin zaɓen.

Wannan hukuncin na zuwa ne bayan wata babbar kotun tarayya da ke Kano a ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Simon Amobeda, ta dakatar da gudanar da zaɓen.

Kara karanta wannan

Kano: Duk da kotu ta taka birki, Hukumar KANSIEC na shirin zaben Ranar Asabar

Sai dai hukuncin da babbar kotun jihar ta yanke a yanzu ya ba da damar gudanar da zaɓen kamar yadda aka tsara.

Kotu ta hana ƴan NNPP takara a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun tarayya ta kori ƴan takarar NNPP 44 a zaɓen ƙananan hukumomin jihar Kano da aka shirya gudanarwa.

Kotun wanda ke zamanta a Kano ta kori dukkan ƴan takarar ciyaman na jam'iyyar NNPP a zaɓen da aka shirya yi ranar Asabar, 26 ga watan Oktoba, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng