Gwamna Ya Zama Na Farko a Arewa da Ya Amince da N80,000 a Matsayin Sabon Albashi
- Gwamna Umaru Bago na Neja ya amince da N80,000 a matsayin sabon albashi mafi ƙaranci ga ma'aikatan jihar
- Bago ya sanar da haka ne bayan ganawa da shugabannin ƙungiyoyin kwadago reshen jihar Neja a fadar gwamnatinsa
- Gwamna Bago ya zama na farko a Arewa da ya kai sabon albashi N80,000 bayan jihohin Legas da Akwa Ibom
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Niger - Gwamna Muhammed Umaru Bago na Neja ya amince da N80,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata a jihar.
Gwamnan ya kuma ba da umarnin fara biyan ma'aikata sabon albashin daga watan Nuwamba, 2024.
Mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin midiya, Abdulbaqy Usman Ebbo ne ya sanar da hakan a shafinsa na X yau Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga dukkan alamu gwamnan zai kasance na farko daga arewacin Najeriya da ya bayyana N80,000 a matsayin mafi karancin albashi a jiharsa.
Gwamna Bago ya gana da ƴan kwadago
Rahotanni sun nuna cewa Gwamna Bago ya sanar da sabon albashin ne bayan wata ganawar sirri da ya yi da kungiyoyin kwadago a jihar.
Ya ƙara da cewa sabon mafi karancin albashin zai taimakawa ma’aikata a jihar, sannan zai ƙara tallafin da yake bai wa ma’aikata ta hanyoyin bunkasa noma.
Idan baku manta ba gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin kwadago na ƙasa sun amince N70,000 ta zama sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa.
Yadda gwamnoni suka fara ƙarin albashi
Sai dai duk da haka wasu gwamnoni sun nuna cewa jihohinsu ba su da ƙarfin tattalin arzikin da za su biya ma'aikata sama da wannan adadi na N70,000.
Jihohin Kudu kamar Legas da Ribas sun bayyana N85,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi, yayin da Enugu da Akwa Ibom suka amince da N80,000.
Amma Gwamna Bogu ya shiga gaba, ya zama gwamnan Arewa na farko da ma’aikata za su karɓi mafi karancin albashi na N80,000 zuwa sama.
Gwamna Kebbi ya sanar da sabon albashi
A wani rahoton kuma gwamnan Kebbi, Nasir Idris ya amince zai biya ma'aikatan gwamnatin jihar mafi ƙarancin albashin wanda ya fi N70,000.
Mai girma Gwamna Nasir Idris ya amince zai biya ma'aikatan jihar sabon mafi ƙarancin albashi na N75,000 duk wata.
Asali: Legit.ng