Kano: Abba Ya Kaɗu da Rasuwar Babban Ɗan Hadiminsa a Kasar Indiya
- Gwamnan jihar Kano ya tura sakon ta'aziyya bayan rashi da aka yi wa darkatan yada labaran gwamnatin jihar a ranar Alhamis
- Daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya rasa dansa mai suna Abubakar Sadik bayan jinya
- Yan uwa da abokan arziki daga sassa daban daban a Najeriya sun taya Sanusi Dawakin-Tofa jimamin rasa dansa da ya yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya shiga cikin yan uwa da abokan arziki wajen yin jaje ga Sanusi Bature Dawakin-Tofa.
A ranar Alhamis Daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya rasa babban dansa.
Abba Kabir Yusuf ya wallafa sakon ta'aziyya ga Sanusi Bature Dawakin-Tofa ne a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba ya yi ta'aziyya bayan rashin Dawakin Tofa
Abba Kabir Yusuf ya nuna damuwa kan rashin da aka yi wa daraktan yada labaran gwamnatinsa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa.
Abba Kabir Yusuf ya ce ya tura ta'aziyya ne ga Sanusi Bature Dawakin-Tofa a madadinsa da gwamnatin Kano.
"Rasuwar yaro matashin lallai abin bakin ciki ne matuka.
Sai dai muna ba kanmu hakuri bisa ƙaddara cewa ya koma ga rahamar Allah.
Ina rokon Allah ya sanya shi a Aljannar Firdausi. Amin"
-Abba Kabir Yusuf
Yaushe za a yi jana'izar Abubakar?
Rahotonni sun nuna cewa a ranar Asabar, 26 ga Oktoba za a yi sallar gawar marigayi Abubakar Sadik Sanusi a Kano.
Za a dauki lokaci kafin sallar gawar ne saboda marigayin ya rasu ne a kasar Indiya bayan jinya da ya yi a can.
Abubakar Saqik ne babban ɗan Sanusi Bature Dawakin-Tofa kuma ya rasu yana da shekaru 15 da haihuwa.
Sanusi II ya je jaje jihar Jigawa
A wani rahoton, kun ji cewa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya kai ziyarar jaje jihar Jigawa bayan hadarin tankar man fetur.
Muhammadu Sanusi II ya gana da gwamnan Jigawa, Umar A. Namadi a fadar gwamnatin jihar tare da rakiya daga masarautar Dutse.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng