'Idan da Ina Son Wa'adi na 3, da Na Yi': Tsohon Shugaban Kasa, Obasanjo Ya Bugi Kirji

'Idan da Ina Son Wa'adi na 3, da Na Yi': Tsohon Shugaban Kasa, Obasanjo Ya Bugi Kirji

  • Tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya yi fatali da rade-radin da ake cewa ya nemi wa'adi na uku a karshen mulkinsa
  • Obasanjo ya ce kwata-kwata a lokacin bai nemi hakan ba, ya ce idan yana so hakan ya fi komai saukin samu a gare shi
  • Tsohon shugaban kasar ya kuma bayyana yadda gwamnatinsa a wancan lokaci ta yi bakin kokari wurin rage basukan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yi magana kan jita-jitar neman wa'adin na uku.

Olusegun basanjo ya kore rade-radin cewa ya nemi wa'adi na uku a lokacin mulkinsa daga 1999 zuwa 2007.

Kara karanta wannan

Ana matsalar lantarki. 'yan Arewa sun dura kan Tinubu, sun ragargaje shi

Obasanjo ya yi magana kan zarginsa da neman wa'adi na 3 a mulkinsa
Olusegun Obasanjo ya ƙaryata jita-jitar cewa a lokacin mulkinsa ya nemi wa'adi na 3. Hoto: Cif Olusegun Obasanjo.
Asali: Getty Images

Obasanjo ya magantu kan neman wa'adi na 3

Obasanjo ya bayyana haka a cikin wani faifan bidiyo yayin hira da News Central TV da Tribune ta bibiya a jiya Alhamis 24 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban kasar ya ce da ya so samun wa'adi na uku da tuni an wuce wurin, ya ce kawai daman bai bukata ba ne.

Ya ce da a ce yana bukatar wa'adi na uku da ya yi ba kamar yadda ake yadawa cewa ya rasa damar ne a lokacin ba.

"Idan ina son wa'adi na uku zan samu, kawai a lokacin ba na bukatar hakan ne, na san gwamnonin da suka yi aiki kan haka, na tabbata idan ni a matsayin shugaban kasa na samu, su ma za su samu."

- Olusegun Obasanjo

Obasanjo ya fadi yadda ya ceto Najeriya

Kara karanta wannan

Raba kasa: Dattijon Arewa, Tanko Yakasai ya hango makomar Najeriya

Obasanjo ya koka kan yadda basuka suka yi yawa ga gwamnatin Najeriya ba tare da kokarin dakile hakan ba.

Ya ce lokacin mulkinsa ya yi iya bakin kokari a rage basukan wurin tattaunawa da kasashe daban-daban.

Obasanjo ya yabawa rayuwa Janar Gowon

Mun ba ku labarin cewa Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya kira sunan Janar Yakubu Gowon musamman, ya yaba masa.

Obasanjo ya ce yana kishi da Janar Gowon saboda yadda ake yabonsa tun bai mutu ba bayan shugabancin Najeriya na tsawon shekaru.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.