Kaico: Ɗalibai 2 Sun Mutu a Wani Harin Kwantan Bauna, Mutane Sun Shiga Jimami

Kaico: Ɗalibai 2 Sun Mutu a Wani Harin Kwantan Bauna, Mutane Sun Shiga Jimami

  • Ɗalibai biyu sun rasa rayukansu da wasu miyagun ƴan bindiga suka kai harin kwantan ɓauna a ƙaramar hukumar Barkin Ladi a Filato
  • Rahotanni sun nuna cewa maharan sun harbe ɗaliban a lokacin da suke har zuwa cikin garin Barkin Ladi, sun kuma ɗauke wayarsu
  • Haka nan kuma an samu labarin cewa wasu miyagu sun burma wa wani mutumi wuƙa a kauyen Kwi duk a jihar Filato

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Plateau - Rahotanni sun ce an kashe dalibai biyu a kusa da ƙauyen Kurra da ke gundumar Gashish a karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Filato.

Daya daga cikin daliban, mai suna Obadiah Daryan ɗan kimanin shekaru 25 yana karatu ne a makarantar koyon kiwon lafiyar dabbobi watau NVRI.

Kara karanta wannan

Tsohuwar Minista ta taimaka wajen samo $57.5bn domin kafa Biafara? Gaskiya ta fito

Taswirar jihar Plateau.
Yan bindiga sun kashe dalibai 2 a jihar Filato Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ɗayan kuma kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Ezekiel Monday ɗan kimanin shekaru 21, dalibi ne a makarantar sakandare ta gwamnati (GSSS) da ke Gashish.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ɗaliban suka rasa ransu a Filato

An tattaro cewa ‘yan bindigar sun yi musu kwanton bauna sannan suka harbe har lahira yayin da suke kan babur za su je garin Barkin Ladi.

Haka nan kuma bayan harbin daliban maharan sun tafi da wayar salula ta ɗaya daga cikinsu, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

An ce bayan kisan ɗaliban kuma wasu miyagu sun ɗabawa wani mai suna, Francis Samuel wuƙa a kauyen Kwi ranar Alhamis da daddare.

Bayanai sun nuna cewa yanzu haka mutumin na kwance a asibiti ana masa magani bayan faruwar lamarin.

Ƴan sanda sun yi shiru kan lamarin

Har kawo yanzu da muke haɗa wannan rahoton jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Filato, Alfred Alabo bai ce uffan ba kan hare-haren.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da manoma, sun sace kayan abinci

Jihar Filato ta jima tana fama da hare-hare, kashe-kashe, lalata gonaki da satar shanu sakamakon rikicin manoma da fulani makiyaya a wasu yankuna.

Mutum 19 sun rasu a haɗari a Filato

A wani labarin kuma kun ji cewa wata motar bas mai ɗaukar fasinjoji 18 ta gamu da mummunan hatsari a yankin ƙaramar hukumar Riyom a jihar Filato.

Mai magana da yawun hukumar kiyaye haɗurra (FRSC), Peter Yakubu ya ce dukkan fasinjojin motar da direba sun mutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262