Bankin CBN Ya Yi Magana kan Lokacin Daina Amfani da Tsofaffin Kudi

Bankin CBN Ya Yi Magana kan Lokacin Daina Amfani da Tsofaffin Kudi

  • Babban bankin Najeriya (CBN) ya fitar da sanarwa kan maganar maye gurbin tsofaffin kudin da sababbin da aka buga
  • Majalisar wakilai ce ta buƙaci babban bankin da ya yi kokarin tsame tsofaffin takardun kudin da suke yawo a Najeriya
  • A lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne aka canza wasu daga cikin takardun kudin kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya yi magana kan amfani da tsofaffin takardun kudi a kasar nan.

CBN ya yi magana ne bayan an fara ce-ce-ku-ce kan halascin amfani da tsofaffin takardun kudi a tarayyar Najeriya.

CBN Naira
CBN ya ce za a iya amfani da tsofaffin kudi. Hoto: Central Bank of Nigeria|Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta ruwaito cewa mukaddashin darektan yada labaran CBN, Sidi Hakama ce ta yi bayani ga yan Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya su shirya: Majalisa ta ba CBN sabon umarni na janye tsofaffin Naira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a cigaba da aiki da tsofaffin kudi - CBN

Daily Trust ta wallafa cewa bankin CBN ya tabbatar da cewa yan Najeriya za su cigaba da amfani da sababbi da tsofaffin takardun kudi.

Mukaddashiyyar darkatar yada labaran CBN, Sidi Hakama ta ce ba a fitar da wata doka da ta nuna haramcin tsofaffin kudin ba.

Sidi Hakama ta kara da cewa babu wata rana, wata ko shekara da aka kayyade kan cewa za a daina karbar tsofaffin takardun kudin.

Ga abin da ta ce:

"Har yanzu ba a soke dokar da kotun tarayya ta yi kan amfani da tsofaffin kudi ba.
Maganar daina karbar tsofaffin kudi ba ta da asali, so ake a kawo ruɗani a Najeriya kawai."

- Sidi Hakama

Bankin CBN ya yi kira gan yan Najeriya

Bayan tabbatar da amfani da tsofaffin takardun kudin, bankin CBN ya bukaci a rika amfani da su da kyau.

Kara karanta wannan

Tattalin arziki: Gwamnati ta fadi yadda za a hana Dala tashi kan Naira

CBN ya ce kyautata rikon takardun kudin zai taimaka wajen kare martabarsu da kuma dadewa ba tare da lalacewa ba.

Najeriya ta yi magana kan dabarun IMF

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta shawarci sauran kasashe cewa ba a kowane lokaci za su yi na'am da shawarar IMF ba.

Ministan Kudi da tattalin arziki, Wale Edun ya bayar da shawarar a Washington DC inda ya halarci taron asusun ba da lamuni da bankin duniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng