Matsalar Lantarki: TCN Ya Fadawa Yan Arewa Gaskiya kan Halin da za a Shiga

Matsalar Lantarki: TCN Ya Fadawa Yan Arewa Gaskiya kan Halin da za a Shiga

  • Kamfanin rarraba lantarki na kasa (TCN) ya yi magana kan yadda wuta za ta cigaba da kasancewa a Arewa
  • TCN ya ce akwai yiwuwar cigaba da samun matsalar wutar lantarki a Arewacin Najeriya saboda wasu dalilai
  • Legit ta tattauna da wani mai injin nika, Muhammad Bashir domin jin halin da suke ciki a halin rashin wuta a Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Arewa - Kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa (TCN) ya bayyana yadda matsalar tsaro za ta cigaba da kawo rashin wutar lantarki a Arewa.

TCN ya ce ko da an gyara wutar lantarki a Arewacin Najeriya a yanzu ba lallai matsalar ta kare baki daya ba.

Kara karanta wannan

Yadda masu caji ke samun alheri sakamakon lalacewar lantarki a jihohin Arewa

Lantarki
TCN ya fadi dalilin cigaba da samun matsalar lantarki a Arewa. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa jami'ar TCN, Injiniya Nafisatu Asabe ce ta bayyana halin da ake ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin rashin wutar lantarki a Arewa

Injiniya Nafisatu Asabe ta bayyana cewa yan bindiga ne suka lalata turken wutar da ya ke kai lantarki Arewacin Najeriya da ke Shiroro.

Biyo bayan lamarin sai aka canza layin wutar Arewa zuwa turken wuta na Ugwuaji-Apir 330kV da ke jihar Benue wanda ya samu matsala a ranar Litinin.

Dalilin rashin gyara layin wutar Shiroro

Daily Post ta wallafa cewa Injiniya Nafisatu Asabe ta ce rashin tsaro ne ya hana TCN gyara layin wutar Shiroro da ke ba Arewa lantarki sosai.

Ta bayyana cewa sun tanadi kayan aiki amma sai suka samu bayanai daga ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro a kan hadarin da ke wajen.

Kara karanta wannan

An yi nasarar gano matsalar lantarki a Arewa, TCN ya yi karin haske

Zancen gaskiya kan lantarki a Arewa

Kamfanin TCN ya bayyana cewa rashin tsaro na cikin abubuwan da ke zama baraza ga yan Arewa a kan samun lantarki.

Injiniya Nafisatu Asabe ta kara da cewa ko da an gyara layin wutar Ugwuaji-Apir ba lallai wuta ta wadata a Arewa ba.

A cewar TCN, a yanzu haka Arewa da kasar Nijar suna haɗaka ne a kan wuta mega 250 kuma idan aka gyara layin Ugwuaji-Apir zai dawo mega 350 ne wanda hakan ba zai wadatar ba.

Legit ta tattauna da Muhammad Bashir

Wani mai injin nika, Muhammad Bashir ya zantawa Legit cewa rashin wuta ya saka ko na abinci ba su samu.

Muhammad Bashir ya ce idan aka cigaba a haka bai san inda zai saka kansa ba kasancewar da aikin nika ya dogara.

Ya ce da shi da dukkan iyalansa da masu sana'a irin ta shi suna cikin wani yanayi maras dadi a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Duk da Dala ta haura N1600, IMF ya yabi kokarin CBN, ya yi ikirarin Naira ta mike

TCN na kokarin gyara wutar Arewa

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin TCN ya fara gyara wutar lantarki da ta samu matsala a jihohin da ke Arewacin Najeriya.

Kamfanin TCN ya ce ya gano wata matsala ce a layin wutan lantarki na Ugwuaji-Apir da ke jihar Benue a Arewacin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng