An Yi Hargitsi a Majalisa, Sanatoci Sun Samu Sabani kan Kudin Hukumomin Raya Shiyya
- An samu hargitsi a majalisar dattawa da aka gabatar da shawarar hanyar samawa hukumomin shiyya kudin gudanarwa
- Takaddamar dai ta taso ne yayin da majalisar dattawa da ta wakilai suka gabatar da kudurin dokokokin kafa hukumomin
- An samu sanatocin da suka nuna rashin amincewa da tsakurar kudin jihohi wajen daukar nauyin sababbin hukumomin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A ranar Alhamis ne aka yi taho-mu-gama a zauren majalisar dattijai kan hanyoyin samar da kudaden za a rika rabawa hukumomin raya shiyya.
Hargitsin da ya barke a majalisar dattawan ya biyo bayan kafa ma’aikatar bunkasa shiyyoyi da shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi.
An samu takaddama a majalisar dattawa
Takaddamar dai ta taso ne a daidai lokacin da majalisar dattawa da ta wakilai suka gabatar da dokar kafa wadannan hukumomin, inji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatoci sun samu sabanin ne a lokacin da aka yi wa kudurin dokar kafa hukumar raya Kudu-maso-Kudu ta 2024 bitar kwakwaf.
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa kudurin dokar kafa hukumar Kudu maso Kudu ne zai zamo samfurin tsari ga sauran hukumomin shiyyoyin kasar.
Kwamitin majalisar dattawa kan ayyuka na musamman ya ba da shawarar tsakuro 15% na kudin da ake baibwa jihohin kowace shiyya domin gudanar da a ayyukan hukumomin.
Sabani kan samar da kudin hukumomi
Sanatoci da dama da suka hada da Yahaya Abdullahi (PDP, Kebbi ta Arewa), Wasiu Eshinlokun (APC, Legas ta Gabas) da Seriake Dickson (PDP, Bayelsa ta Yamma), sun nuna damuwarsu a fili.
Sanata Abdullahi ya yi gargadin cewa wannan tanadin zai iya haifar da kalubalen shari’a daga gwamnatocin jihohi, domin babu wata jiha da ta yarda a rage mata kason da ta ke samu.
Da yake martani kan lamarin, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya bayyana cewa kashi 15 na kasafin kudin ba zai shafi kudaden jihohin kai tsaye ba.
Duk da bayanin da Barau ya yi, wasu sanatoci da dama sun nuna rashin gamsuwarsu da tsarin.
Sai dai shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio ya shigo cikin lamarin, ya yi kira da a kada kuri’a, kuma masu rinjaye sun amince da tanadin.
Majalisa ta amince da kafa hukumar NWDC
A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar dattawa ta amince da kudirin dokar kafa hukumar raya shiyyar Arewa Maso Yamma bayan rahoton kwamiti.
Sanata Kaka Shehu, shugaban kwamitin ayyuka na musamman ya gabatar da rahoto kan kudurin, ya ce hukumar za ta taimaka wajen bunkasa shiyyar.
Asali: Legit.ng