Tsohuwar Minista Ta Taimaka Wajen Samo $57.5bn Domin Kafa Biafara? Gaskiya Ta Fito

Tsohuwar Minista Ta Taimaka Wajen Samo $57.5bn Domin Kafa Biafara? Gaskiya Ta Fito

  • Wani rahoto da ke yawo a soshiyal midiya ya nuna cewa masu fafutukar kafa ƙasar Biafara sun samo $57.5bn domin kafa gwamnati
  • Rahoton da aka jinginawa jagoran ƴan aware Simon Akpa ya yi ikirarin tsohuwar minista Ngozi Okonjo-Iweala ta taimaka wajen samo kuɗin
  • Legit Hausa ta gano wannan raɗe-raɗe ba gasƙiya ba ne kuma shugabar WTO da Ekpa sun nesanta kansu da rahoton duk da shahararsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta musamman X ya yi ikirarin cewa ƴan aware sun samu tallafin Dala biliyan 57.5 domin kafa gwamnatin Biafara.

Wannan ikirari da ake zargin yana da alaka da Simon Ekpa, wanda ya ayyana kansa a matsayin jagoran fafutukar neman kafa kasar Biafra, ya dade yana yawo a soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

Yadda masu caji ke samun alheri sakamakon lalacewar lantarki a jihohin Arewa

Dr. Ngozi Okonjo-Iweala da Simon Ekpa.
Rade-raden an ba ƴan aware $57.5bn domin kafa gwamnatin Biafara ba gaskiya ba ne Hoto: Bloomberg/Simon Ekpa
Asali: Getty Images

Bugu da ƙari, masu yaɗa jita-jitar sun nuna cewa shugabar kungiyar WTO ta duniya, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta ba da gudummuwa wajen samo maƙudan kuɗin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan aware na ɗaya daga cikin matslolin da Najeriya ke fam da su, inda wasu tsiraru ke fafutukar ɓallewa daga Najeriya da kafa kasar Biafara.

Ƙungiyar ƴan aware watau IPOB na ci gaba da wannan fafutuka a shiyyar Kudu maso Gabas, inda take ƙaƙabawa mutane dokoki da kai hare-hare kan jami'an tsaro.

Gwamnatin Najeriya dai ta haramta wannan ƙungiya kuma ta kama shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, kan zarge-zargen ta'addanci da cin amanar ƙasa.

Menene gaskiyar kudin kafa gwamnatin Biafara?

Da farko dai Darakta Janar ta kungiyar kasuwanci ta duniya WTO, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta karyata zargin tana da hannu wajen samo $57.5bn don kafa gwamnatin Biafara.

Tsohuwar ministar ta bayyana hakan ne a shafinta na X yayin da take martani kan labarin da ke yawo na kafa gwamnatin ƴan aware watau Biafara.

Kara karanta wannan

Kaico: Ɗalibai 2 sun mutu a wani harin kwantan ɓauna, mutane sun shiga jimami

Ta jaddada cewa maganar gaba daya kage ce, sannan ta bukaci masu amfani da sunanta a irin wannan ƙagaggen labarin mara tushe da su daina.

Da take maida martani Okonjo-Iweala ta ce:

"Na san babu wani mai hankali da zai yarda da abin da ke kunshe a wannan saƙon da ke ƙasa, amma duk da haka yana da muhimmanci na fito na tabbatar da cewa ƙarya ce."
"Haka kuma ina kira ga waɗnda ke kokarin amfani da sunana su shiga taitayinsu, ka da su ƙara sani a ciki."

Simon Ekpa ya maida martani ga Dr. Ngozi

Bayan da Okonjo-Iweala ta tsame kanta, Simon Ekpa ya fitar da sanarwa a shafin X, inda ya musanta cewa shi ne ya fara yaɗa jita-jitar samun kuɗin.

Ekpa ya kara da cewa bai yi ikirarin da ake zarginsa da shi ba, yana mai bayyana hakan a matsayin "karya mara tushe."

Ya kuma caccaki Okonjo-Iweala kan yadda ta yi shiru kan batutuwan da suka shafi tashe-tashen hankula da kashe-kashe a Najeriya, musamman a yankin Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya aika muhimmin saƙo ga ministoci 5 da ya kora daga aiki

Ekpa, wanda ya yi fice wajen goyon bayan fafutukar kafa kasar Biafra da kuma sukar gwamnatin Najeriya, ya mayar da martani da cewa:

"Ba ni na wallafa wannan labarin ba, abin mamaki yau ga shi kina magana saboda an sa sunanki, duk maganar da muke kan ta'addancin da ake wa ƙabilarki ba ki taɓa cewa komai ba."

Bisa wannan dai ta tabbata cewa raɗe-raɗen cewa ƴan aware sun samu tallafin Dala biliyan 57.5 domin kafa gwamnati ba gaskiya ba ne.

An shawarci ƴan Arewa kan raba Najeriya

A wani labarin kuma Farfesa Abubakar Sani Lugga ya yi magana kan kiraye-kirayen da yan Kudu ke yi game da raba Najeriya.

Farfesan ya shawarci al'ummar yankin Arewa da su hada kai, su fara dogaro da kai domin tsayawa da kafarsu tun kafin a raba ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262