Buhari da Tinubu: Yadda Tushen Wutar Lantarkin Najeriya Ya Lalace sau 105
- Duk da cika shekaru 64 da samun yancin kai, har yanzu ana cigaba da samun matsalar lantarki a dukkan sassan Najeriya
- A tsakanin lokacin mulkin Muhammadu Buhari da Bola Ahmed Tinubu an samu lalacewar tushen wutar Najeriya sau 105
- A wannan rahoton, mun tattaro muku yadda tushen wutar lantarkin ya lalace a lokutan mulkin APC duk da alkawarin gyara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - A tsawon shekaru, yan Najeriya a birane da ƙauyuka na cigaba da kokawa kan matsalar wutar lantarki.
Tun fara mulki APC da suka yi alkawarin kawo canji a Najeriya, an samu lalacewar tushen wutar Najeriya sau 105.
A wannan rahoton, mun tattaro muku yadda tushen wutar ya lalace a lokutan mulkin Muhammadu Buhari da Bola Ahmed Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayani kan tushen wutar lantarkin Najeriya
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa tushen wutar lantarkin Najeriya wanda a turance ake kira da National Grid ne ke tura wuta ga kamfanonin da ke rarrabawa al'umma.
Hukumar NERC ta bayyana cewa an tsara tushen wutar lantarkin ne ya yi aiki a kan ƙarfin wuta da ya kai 330kV ± 5.0 da 50Hz ± 0.5
Duk lokacin da aka samu tushen wutar ya yi kasa da yadda aka tsara shi zai dakatar da harba wuta ga sassan kasa kuma za a shiga dubu.
Lalacewar tushen wuta a mulkin Buhari
Jaridar Punch ta yi rahoto kan cewa a mulkin Muhammadu Buhari an samu lalacewar tushen wutar lantarki har sau 93.
1. 2015
Bayan Muhammadu Buhari ya karbi mulki a shekarar 2015, an samu lalacewar tushen wutar lantarki sau uku.
2. 2016
A cikin shekara ta biyu a mulkin Buhari, an samu lalacewar tushen wutar Najeriya har sau 28.
3. 2017
A shekarar 2017 an samu lalacewar tushen wutar lantarki sau 24 a karkashin mulkin Buhari.
4. 2018
Tushen wutar lantarkin Najeriya ya lalace har sau 13 a shekarar 2018 da Buhari ya fara shirin tazarce.
5. 2019
A shekarar 2019 Buhari ya samu mulki karo na biyu kuma tushen wutar lantarki ya lalace har sau 11.
6. 2020 zuwa 2023
A tsakanin shekarun 2020 zuwa 2023 an samu sauƙin lalacewar tushen wutar lantarki kamar yadda rahoton Premium Times ya nuna.
A tsakanin shekarun, tushen wutar ya lalace ne sau 14 har Buhari ya kammala mulki a ranar 29 ga watan Mayu na 2023.
Lalacewar tushen wuta a mulkin Tinubu
Tushen wutar Najeriya ya cigaba da lalacewa bayan Bola Tinubu ya karbi mulki daga hannun Muhammadu Buhari.
Daga fara mukin Bola Tinubu, tushen wutar lantarkin Najeriya ya lalace sau 12.
1. 2023
Daga karɓar mulkin Bola Tinubu a shekarar 2023, an samu lalacewar tushen wutar lantarki har sau uku.
Lalacewar lantarkin ta faru ne a tsakanin watannin Yuni zuwa Disamba a shekarar 2023.
2. 2024
Bayan Bola Tinubu ya shiga shekara ta biyu a 2024, an samu lalacewar tushen wutar lantarki har sau tara.
A makon da ya wuce tushe wutar ya lalace har sau uku a cikin mako daya wanda hakan ya saka yan Najeriya korafi.
Matsalolin lantarki a mulkin Tinubu
Bayan lalacewar tushen wutar lantarki, an samu karin wasu matsalolin wuta a mulkin Bola Tinubu musamman a Arewa.
Wasu jihohin Arewa maso Gabas sun shafe watanni babu wuta sakamakon lalata turken wuta da yan ta'adda suka yi.
Haka zalika lalacewar wutar ya taba shafar jihohin Borno da Yobe a lokacin da Boko Haram suka lalata turken wuta.
A ranar Litinin da ta wuce aka samu lalacewar turken wuta wanda ya jefa al'ummar Arewa cikin duhu.
Ana ƙoƙarin gyara wutar Arewa
A wani rahoton, mun ruwaito muku cewa kamfanin TCN ya ce ya yi nasarar gano inda wutar lantarkin Arewa ta samu matsala a jihar Benue.
Tun bayan gano matsalar, TCN ya ce ya tura injiniyoyi domin su fara aikin maido da lantarki a sassan Arewacin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng