Kamfanin MTN Ya Yi Asarar Naira Biliyan 11 a cikin Watanni 12, An Gano Dalilin Rashin

Kamfanin MTN Ya Yi Asarar Naira Biliyan 11 a cikin Watanni 12, An Gano Dalilin Rashin

  • Kamfanin IHS da ke kula da kadarorin mafi akasarin kamfanonin sadarwa a kasar nan ya fitar da rahoto kan asarar da MTN ya yi
  • Rahoton IHS ya nuna cewa kamfanin MTN ya yi asarar Naira biliyan 11 a cikin watanni 12 sakamakon lalacewar wayoyin sadarwa
  • An ce biliyoyin Naira da MTN ya rasa ya isa ya ba kamfanin damar gina kilomita 870 na wayoyin sadarwa a wuraren da ba a samunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Katsewar sama da wayoyin sadarwa 6,000 a tsakanin shekarar 2022 zuwa 2023 ya jawo kamfanin MTN na Najeriya ya yi asarar Naira biliyan 11.

Kamfanin IHS da ke kula da kadarorin mafi akasarin kamfanonin sadarwa a kasar nan ne ya fitar da rahoton asarar da MTN ya yi.

Kara karanta wannan

An gano ma'aikatan NNPCL a cikin wadanda hatsarin jirgi ya rutsa da su a Ribas

Kamfanin IHS ya yi magana kan asarar da MTN ya yi a cikin shekara daya
Kamfanin MTN ya yi asarar Naira biliyan 11 sakamakon lalacewar wayoyin sadarwa. Hoto: Waldo Swiegers
Asali: Getty Images

MTN ya yi asarar N11bn a watanni 12

IHS ta ce kamfanin na MTN ya gyara kilomita 2,500 na wayoyin sadarwar masu rauni a kan kudi sama da Naira biliyan 11 a cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton IHS ya nuna cewa kudin da MTN ya kashe sakamakon lalacewar wayoyin ya isa ya gina sababbin wayoyin na kilomita 870 a wuraren da ba sabis.

Ba tun yanzu ba ake ta yin kira ga gwamnatin tarayya da ta ayyana kadarorin sadarwa a matsayin muhimmin kadarorin kasa domin magance hare-haren da ake kai masu.

Bukatun kamfanonin sadarwa ga gwamnati

Manyan masu ruwa da tsaki a fannin sun kuma bukaci gwamnati da ta kare kadarorin sadarwar Najeriya daga kutsen intanet, sata da masu barna.

Sun kuma bukaci gwamnati da ta dauki nauyin kula da tsaron kadarorin sadarwa, wadanda a yanzu aka ayyana su a matsayin mahimman kadarori na kasa.

Kara karanta wannan

An yi nasarar gano matsalar lantarki a Arewa, TCN ya yi karin haske

Wadannan masu ruwa da tsaki sun hada da kamfanonin kula da kadarorin sadarwa, kamar IHS Towers, kungiyar kamfanonin sadarwa ta Najeriya da kuma hukumar sadarwar Najeriya.

MTN ya rufe ofisoshinsa na Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa katafaren kamfanin sadarwa na MTN, ya rufe dukkanin ofisoshi da cibiyoyinsa da ke a fadin Najeriya.

An rahoto cewa MTN bai bayyana dalilin rufe ofisoshinsa ba amma ana kyautata zaton ba ya rasa nasaba da fargabar farmaki daga jama'a ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.