An Buƙaci Tinubu Ya Kara Korar Ministoci, An Kawo Sunayen Wasu
- Biyo bayan sallaman ministoci biyar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a ranar Laraba, yan Najeriya sun yi martani
- Kungiyoyin ma'aikatu masu zaman kansu sun yi tsokaci kan matakin da shugaban kasa Bola Tinubu ya dauka a jiya
- Wasu yan Najeriya sun yi korafi kan korar ministocin, suka ce har yanzu akwai karin waɗanda ya kamata Bola Tinubu ya kora
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Korar ministoci da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na cigaba da jan hankulan yan Najeriya.
Wasu yan Najeriya sun kara kira ga shugaban kasa Bola Tinubu kan kara korar ministoci biyar da ya yi.
Jaridar Punch ta haɗa rahoto a kan martanin da yan Najeriya suka yi bayan korar ministocin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Martanin ma'aikatu masu zaman kansu
Shugaban kungiyar masu kananan sana'o'i na kasa, Dr Femi Egbsola ya ce akwai bukatar duba wasu ministocin da ba su kokari a sallame su.
Dr Femi Egbsola ya kara da cewa idan aka yi dubi ga tattalin Najeriya za a tabbatar da cewa har yanzu akwai sauran aiki.
Shugaban Intellectual Edge Service, Dr Olusegun Ogundare ya ce korar ministoci abu ne mai kyau amma da sake a lamarin Tinubu.
Olusegun Ogundare ya ce akwai bukatar sallamar karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da ministan makamashi, Adebayo Adelabu.
Martanin yan kafar sada zumunta
Yan Najeriya a kafafen sada zumunta sun buƙaci Bola Tinubu ya kara korar wasu ministoci idan da gaske yake.
Wani mai amfani da kafar X, @Imeeeokon ya bukaci a kori ministan Abuja, Nyesom Wike saboda a cewarsa ya gaza.
A ra'ayin @Nwafresh, ministan man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri ya kamata a kora idan da gaske ake.
An soki Tinubu kan korar ministoci
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyun adawa a Najeriya sun yi maratani kan korar ministoci da Bola Tinubu ya yi.
Jam'iyyun PDP, LP da SDP sun ce Bola Tinubu ya kori ministoci biyar ne domin a kawar da hankalin yan kasa kan gazawar da ya yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng