Minista Ya Umarci Sojoji Su Kawo Karshen Ƴan Bindiga, Ya Tashi Tsaye kan Bello Turji

Minista Ya Umarci Sojoji Su Kawo Karshen Ƴan Bindiga, Ya Tashi Tsaye kan Bello Turji

  • Ministan tsaro, Muhamnad Badaru ya ziyarci rundunar sojin Operation Fansar Yamma da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara
  • Badaru ya jinjinawa sojojin bisa namijin kokarin da suka yi a yaƙi da ƴan ta'adda, ya buƙaci su kamo jagoran ƴan bindiga, Bello Turji
  • Badaru ya tabbatar wa sojojin shugabn ƙasa Bola Tinubu ya san kokarin da suke yi kuma zai samar masu da duk abin da ake bukata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara - Ministan tsaro, Mohammad Badaru Abubakar, ya umarci sojojin Operation Fansar Yamma da su kamo ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga, Bello Turji.

Ministan ya bayar da wannan umarnin ne a lokacin da yake jawabi ga sojojin a hedikwatar Birged ta daya da ke Gusau a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya tura sako ga Tinubu awanni bayan raba shi da mukaminsa

Badaru Abubakar.
Ministan tsaro ya umarci sojoji su kamo Bello Turji Hoto: Muhammad Badaru Abubakar
Asali: Facebook

Tinubu ya san halin da ake ciki kan matsalar tsaro

Ministan ya ce shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu yana sane da kokarin da sojoji ke yi kuma ya ga nasarorin da suka samu a ƴan watannin da suka shige, Channels tv ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Badaru ya ce Tinubu ya san halin da ake ciki da nasarorin da sojoji ke ƙara samu a yaƙi da ƴan ta'adda amma duk da haka akwai sauran ƙalubale.

Badaru ya umarci sojoji su kamo Bello Turji

"Bisa haka shugaban ƙasa ya buƙaci na gode muku a madadinsa, sannan yana rokon ku kara zage dantse wajen kawo karshen matsalar tsaro a nan yankin da ƙasa baki ɗaya.
"Shugaban ƙasa a shirye yake ya ba ku duk abin da kuke buƙata don dawo da zaman lafiya a Arewa maso Yamma da Najeriya baki ɗaya. Kwamanda ya ba ni tabbaci kuma na gamsu."

Kara karanta wannan

Jerin ministocin da Tinubu ya kora daga aiki da jihohin da suka fito a Najeriya

"Kun shiya gamawa da su? Kun shirya rufe babin matsalar tsaro? Dan Allah su kamo mani Bello Turji."

- Badaru Abubakar

Ministan tsaro ya ziyarci rundunar Operation Fansar Yamma da ke Gusau domin jin halin da ake ciki game da ayyukan dakarun sojoji, Pulse ta ruwaito.

Ministan ya samu tarba daga kwamandan rundunar hadin gwiwa ta Operation Fansar Yamma, Manjo Janar Oluyinka Soyele, mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mani Mumun, da saurasu.

Najeriya za ta sayo jiragen yaƙi

A wani rahoton kuma gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa za ta ranto Dala miliyan 600 domin sayo manyan jiragen yaki.

Tun a zamanin tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari, gwamnatin kasar nan ta bayyana sha'awar mallakar jiragen hallaka 'yan ta'adda.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262