Kano: Gwamna Ya Bayyana Dalilin Nada Muhammad Maharazu Sarkin Karaye

Kano: Gwamna Ya Bayyana Dalilin Nada Muhammad Maharazu Sarkin Karaye

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya mika sandar mulki ga sabon sarkin Karaye, Alhaji Muhammad Maharazu a ranar Alhamis
  • Gwamna Abba ya ce an nada Sarki Muhammad Mahazaru sarautar ne saboda nagartattun halayensa na gaskiya da rikon amana
  • Hotunan mika sandar da Gwamna Abba ya wallafa sun nuno Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a cikin mahalarta taron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano na ci gaba da mika sandunan sarauta ga sababbin sarakunan masarautu biyar na jihar.

A ranar 23 ga Oktoba, Gwamna Abba ya mika sandar girma ga sabon sarkin Karaye, Alhaji Muhammad Maharazu Karaye.

Gwamna Abba ya bayyana halayen sabon sarkin Karaye, Alhaji |Muhammad
Gwamnan Kano ya mika sandar girma ga sarkin Karaye, Alhaji Muhammad. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Abba ya mika sanda ga sarkin Karaye

Kara karanta wannan

A karshe, Tinubu ya ji korafe korafen yan Najeriya, ya sallami Ministoci 5

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a yammacin Alhamis, 24 ga watan Oktoba, gwamnan Kano ya taya Alhaji Muhammad murnar samun mukamin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na samu karamcin mikawa Mai Martaba Sarkin Karaye Alhaji Muhammad Maharazu Karaye sandar mulki a jiya a garin Karaye."

- A cewar Gwamna Abba.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci bikin mika sandar akwai Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo.

'Muhammad na da amana' - Gwamna

Gwamna Abba ya ce an nada Alhaji Muhammad matsayin sarkin Karaye ne bisa halayensa na gaskiya da rikon amana, yana mai cewa:

"Ina da yakinin cewa zai zamo shugaba na gari kuma abin koyi ga al'ummar masarautarsa.
"Na yi amfani da wannan dama wajen jawo hankalin sabon sarkin da ya yi mulkin da al'umarsa za su yi koyi da shi kuma ya rike kowa bisa adalci."

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa 2 sun sa labule da Minista domin kawo karshen rashin tsaro

Gwamnan ya ce ya na da yakinin cewa Sarki Muhammad zai yi aiki kafada da kafada da sauran sarakunan Kano da domin ciyar da masarautarsa da jiharsa gaba.

Duba hotunan mika sandar a kasa:

An mika sanda ga sarkin Gaya

A wani labarin makamancin wannan, mun rahoto cewa gwamnan Kano, Abba Yusuf ya mika sandar mulki ga sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim.

Gwamna Abba ya ce yana da yakinin cewa Sarki Aliyu zai gaji kyawawan halayen mahaifinsa, marigayi Sarki Ibrahim Abdulkadir ta hanyar yin shugabanci bisa turbar Islama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.