ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Ɗalibai za Su Koma Jami'a
- Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa reshen jihar Gombe ta janye yajin aikin da ta shiga tun a watan Satumban 2024
- ASUU ta sanar da janye yajin aikin ne a wata takarda da ta rubutawa mukaddashin shugaban jami'ar jihar Gombe
- Kungiyar ta hakura bayan tattaunawar da ta riƙa yi da gwamnatin jihar Gombe a kan wasu hakkokin malamai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - Ƙungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) reshen jami'ar jihar Gombe ta sanar da janye yajin aiki.
A yau Alhamis kungiyar ta rubuta takardar janye yajin aikin bayan tattaunawa da ƴaƴanta suka yi a jami'ar Gombe.
Shugaban ASUU na jami'ar jihar Gombe, Dr Sulaiman Salihu Jauro ne ya tabbatar da janye yajin aikin a wata takarda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ASUU ta janye yajin aiki a Gombe
Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) reshen jami'ar jihar Gombe ta janye yajin aikin da ta shiga a ranar 11 ga Satumba.
Shugaban ASUU na jami'ar jihar Gombe, Dr Salihu Sulaiman Jauro ne ya sanya hannu a kan wata takardar janye yajin aikin da kungiyar ta rubuta.
Ga abin da yake cewa:
"Bayan lura da alkawarin da muka yi da gwamnati, dukkan yan kungiyar ASUU sun amince da janye yajin aikin da muka shiga."
-Dr Sulaiman Salihu Jauro, shugaban ASUU
Kungiyar ASUU ta tura takardar janye yajin aikin ga mukaddashin shugaban jami'ar, Farfesa Sani Ahmed Yauta.
Yaushe dalibai za su koma makaranta?
A bisa dukkan alamu dukkan ɗaliban jami'ar jihar Gombe za su koma karatu ne a ranar Litinin mai zuwa.
Sai dai za a jira hukumar makarantar ta fitar da sanarwa a hukumance kamar yadda aka saba duk bayan janye yajin aiki.
Gwamnatin Tinubu za ta sasanta da ASUU
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka tana koƙarin dakile sabon yunkurin malaman jami'a na shiga yajin aiki.
Karamar ministar kwadago, Hon. Nkeiruka Onyejeocha ce ta bayyana hakan a wani taron kiwon lafiya da ta halarta a jihar Abia.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng