Tinubu Ya Tura Wasika ga Majalisa domin Tantance Ministocin da Ya Nada

Tinubu Ya Tura Wasika ga Majalisa domin Tantance Ministocin da Ya Nada

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura takarda ga majalisar dattawan Najeriya domin tantance ministocin da ya zaɓo
  • Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya tabbatar da karɓar wasikar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • A ranar Laraba ne shugaban kasa ya sauke wasu ministoci tare da zaɓen wadanda za su maye gurbinsu a majalisar zartarwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauki mataki na gaba domin tabbatar da ministocin da ya zabo.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura takarda ga majalisar dattawan Najeriya domin tantance sababbin ministocin.

Tinubu
Tinubu ya bukaci tantance ministocin da ya nada. Hoto: Nigerian Senate|Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar the Nation ta wallafa wani hasashe kan ranar da majalisar dattawan Najeriya za ta tantance ministocin.

Kara karanta wannan

Dalilin Bola Tinubu na korar ministoci 5 ya bayyana, an faɗi asalin abin da ya faru

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Bola Tinubu ya sauke ministoci 5

A ranar Laraba ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sauke wasu daga cikin ministocinsa guda biyar.

Lamarin na cikin ƙoƙarin da Bola Tinubu ya ke yi wajen ganin ya gyara tafiyar mulkinsa da kuma kawo cigaba a Najeriya.

Bola Tinubu ya tura takarda ga majalisa

This Day ta ruwaito cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura takarda ga majalisar dattawan Najeriya domin ta tantance sababbin ministoci.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya karanta takardar shugaba Bola Tinubu yayin zaman majalisar na yau.

Yaushe za a ta tantance ministocin Tinubu?

Ana hasashen cewa a ranar Laraba mai zuwa majalisar dattawan Najeriya za ta tantance ministoci bakwai da Bola Tinubu ya tura sunayensu.

A bisa dokar kasa, dole sai majalisa ta tantance mutum kafin ya zama minista a majalisar zartarwar da shugaban kasa ke jagoranta.

Kara karanta wannan

Jam'iyyu sun haɗu sun ragargaji Tinubu kan korar ministoci

An soki Tinubu kan sauke ministoci

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyun adawa sun soki sauya ministoci da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi a ranar Laraba.

Jam'iyyun PDP, LP da SDP sun dura kan Bola Tinubu inda suka ce ba sauya ministoci talakawa ke bukata a Najeriya ba a halin yanzu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng