Majalisa na Shirin Sa a Daure Iyaye kan Rashin Tura Yara Makaranta

Majalisa na Shirin Sa a Daure Iyaye kan Rashin Tura Yara Makaranta

  • Majalisar dokokin kasar nan ta fara shirin daukar matakin da zai magance yadda iyaye ke kin tura yaransu makaranta
  • Matakin ya biyo bayan koken shugaban majalisa, Godswill Akpabio na cewa yara akalla miliyan 20 ba sa zuwa makaranta
  • Kwamitin ilimi a majalisar dattawa ya fara duba yiwuwar bijiro da kudurin da zai bayar da dama a daure wasu iyayen yara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta ce ana kokarin daukar hukunci a kan iyayen da ba sa sanya yaransu a makaranta.

Wannan ya biyo bayan koken da manyan kasar nan ke yi, daga cikinsu har da tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo na yawaitar yara da ba sa makaranta.

Kara karanta wannan

Ana kukan lantarki, ruwa ya karya gadar da ta haɗa ƙauyuka sama da 50

Senate
Majalisa za ta samar da kudurin daure iyaye marasa aika yara makaranta Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Kafar BBC Hausa ta ruwaito cewa kwamitin ilimi na majalisar ya bayar da shawarar daukar matakin shari'a bisa rashin tura yara makarantu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar tarayya na son daure iyayen yara

Shugaban kwamitin ilimi na majalisa, Sanata Lawan Adamu Usman ya ce su na duba yiwuwar bayar da shawarar daure iyayen yara kan rashin aika yaransu makaranta.

“Muna son a yi dokar daurin wata shida ga iyayen da suka ki sanya 'ya'yansu a makaranta.
"Shi ma ilimi masu iya magana na cewa shi ne gishirin rayuwa, kuma shi ne maganin duka matsalolin da ke faruwa a ƙasar nan,"

- Sanata Lawan Adamu Usman.

Majalisa ta damu game da matsalar ilimi

Majalisar dattawan Najeriya ta na son daukar matakin shari'a a kan iyayen saboda yadda ake samun karuwar yara marasa zuwa makaranta.

Mataimakin shugaban majalisar, Barau Jibrin ya ce rashin zuwan yaran makaranta babbar damuwa ce da ta yi kamari a Arewacin kasar nan.

Kara karanta wannan

'Yana yawo cikin dare,' Sanata ya tona yadda Tinubu yake zagaya gari a boye

Majalisa ta fadi adadin marasa zuwa makaranta

A wani labarin kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta bayyana takaicin yadda alkaluma su ka tabbatar da karuwar yara marasa zuwa makaranta.

Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya ce akalla yara miliyan 20 ne aka tabbatar da ba sa zuwa makaranta, wanda hakan babbar barazana ce ga tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.