An Cafke Yan Bindiga Masu Tare Hanya Suna Sace Mutane

An Cafke Yan Bindiga Masu Tare Hanya Suna Sace Mutane

  • Rundunar yan sanda a jihar Rivers ta cafke wasu yan bindiga masu garkuwa da mutane da suka shahara da kai hare hare
  • Ana zargin cewa yan bindigar sun saba sace mutane a kan hanya kuma su suka sace wani mai hidimar kasa kwanan nan
  • Kwamishinan yan sanda na Rivers ya yi karin haske kan ta'addancin da ake zargin miyagun da yawan yi a sassan jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Rundunar yan sandan jihar Rivers ta yi babban kamu yayin da ta fita wani samame na musamman.

Yan sanda sun yi nasarar cafke wasu masu garkuwa da mutane da ake zargi suna tare hanya suna satar mutane.

Kara karanta wannan

Tirelar Dangote ta markaɗa ɗan acaɓa har lahira yayin da suka yi karo

Yan sanda
An kama yan bindiga a Rivers. Hoto Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa rundunar yan sanda ta yi kira na musamman ga al'umma kan lamarin yan bindiga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama yan bindiga a jihar Rivers

Leadership ta ruwaito cewa rundunar yan sanda ta yi nasarar cafke wasu manyan yan bindiga yayin wani farmaki da ta kai kan miyagu.

Kwamishinan yan sandan Rivers, CP Mustapha Muhammad ya bayyana cewa an cafke yan bindigar ne a ranakun 17 da 18 ga Oktoba.

Yadda yan bindiga ke tare hanya a Rivers

Rundunar yan sanda ta bayyana cewa ana zargin cewa yan bindigar na tare hanya kamar jami'an tsaro sai su rika sace mutane.

Kuma ana zargin cewa a kwanan nan sun sace wani mai hidimar kasa watau NYSC da wasu mutane biyu a kan hanya.

Kwamishinan yan sandan ya kara da cewa ana zargin miyagun da kai hare hare da dama a yankunan jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga gari sun bude wuta, da dama sun mutu

Kiran yan sanda ga al'ummar jihar Rivers

CP Mustapha Muhammad ya yi kira ga al'umma kan su cigaba da ba su bayanai da za su taimaka musu wajen kama yan bindiga a jihar.

Kwamishinan ya kuma tabbatar da cewa za su cigaba da bayar da tsaro yadda ya kamata domin kawo karshen yan ta'adda.

An kama yan bindiga a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun ƴan sanda sun kama wasu ƴan bindiga bakwai da suka addabi Abuja da jihohin Kaduna da Neja.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama ya ce kudin fansar da suke karɓa na karewa ne wurin neman matan banza da shaye-shaye.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng