Bobrisky: Dan Daudu Ya Kwana a Asibiti, Ya Ce Nonuwansa na Ciwo, An Samu Bayanai
- Fitaccen dan Daudun nan, Idris Okuneye ya kwana a wani asibiti da ke jihar Lagos saboda rashin lafiya ta gaggawa
- A ofishin yan sanda, Dan Daudun da aka fi sani da Bobrisky ya yi korafi kan wani irin ciwo da yake ji a cikin nonuwansa
- Hakan ya biyo bayan cafke Bobrisky da aka yi tare da kulle shi a ofishin yan sanda da ke Alagbon a jihar Lagos
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - An garzaya da fitaccen dan Daudu, Idris Okuneye zuwa asibiti domin ba shi kulawar gaggawa.
Dan Daudun da aka fi sani da Bobrisky ya kwana a asibiti saboda fama da ciwo da yake a cikin nononsa.
Bobrisky: Dan Daudu ya kwana a asibiti
Vanguard ta tabbatar cewa an kai Bobrisky asibiti ne bayan shafe lokaci mai tsawo a kulle a jihar Lagos.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kulle Bobrisky ne bayan cafke shi da aka yi yana shirin tserewa daga Najeriya inda aka ajiye shi a ofishin yan sanda da ke yankin Alagbon a jihar Lagos.
Motar daukar marasa lafiya ce ta dauki Bobrisky zuwa asibiti a jiya Laraba 23 ga watan Oktoban 2024.
Musabbabin kai dan Bobrisky asibiti a Lagos
Bobrisky ya yi korafi kan yadda yake jin zafi a jikin nonuwansa wanda ya tilasta kai shi asibiti ba tare da wata-wata ba.
Wata majiya ta ce lokacin da yan jaridu suka tambayi sunan dan Daudun yana cikin mota ya fada musu sunansa na maza.
A cikin motar daukar marasa lafiya, an gano wata mai kula da lafiyarsa da kuma jami'an tsaro da ke gadinsa, Leadership ta ruwaito wannan.
An cafke Bobrisky yana shirin tserewa
Kun ji cewa an kara samun bayanai kan yadda aka cafke Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky yana shirin guduwa daga kasar.
Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa an cafke Idris Okuneye ne da tsakar dare yana ƙoƙarin tsallake iyakokin Najeriya da Benin.
Hukumar shige da ficen Najeriya (NIS) ce ta cafke Bobrisky kuma ta bayyana matakin da za ta dauka a kansa bayan an maido shi gida.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng