Tsohon Minista Ya Tura Sako ga Tinubu Awanni bayan Raba Shi da Mukaminsa

Tsohon Minista Ya Tura Sako ga Tinubu Awanni bayan Raba Shi da Mukaminsa

  • Abdullahi Tijjani Gwarzo ya aika saƙo ga shugaban ƙasa Bola Tinubu bayan guguwar garambawul ta ritsa da shi
  • Tsohon ƙaramin ministan na gidaje da raya birane ya nuna godiyarsa ga shugaba Bola Tinubu bisa damar da ya ba sa
  • Ya yi fatan alheri tare da samun nasara ga wanda zai maye gurbinsa a kujerar da ya rasa a bayan taron FEC a ranar Laraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya yi magana bayan ya rasa muƙaminsa a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Tsohon ministan dai yana ɗaya daga cikin ministoci biyar da shugaba Tinubu ya sallama a garambawul ɗin ya yi ranar Laraba, 23 ga watan Oktoban 2024.

Kara karanta wannan

Dalilin Bola Tinubu na korar ministoci 5 ya bayyana, an faɗi asalin abin da ya faru

Gwarzo ya tura sako ga Tinubu
Abdullahi T Gwarzo ya nuna godiyarsa ga Tinubu Hoto: @ATMgwarzo
Asali: Twitter

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na X jim kaɗan bayan raba shi da muƙaminsa, tsohon ministan ya nuna godiyarsa kan damar da aka ba shi ta yi wa Najeriya hidima.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me tsohon ministan ya ce ga Tinubu?

Gwarzo ya nuna godiyarsa kan damar da shugaban ƙasa ya ba shi domin ba da irin ta shi gudunmawar wajen kawo ci gaba a Najeriya.

Ya bayyana cewa duk da bai ɗauki dogon lokaci a muƙamin ba, yana alfahari da ci gaban da ya samu da kuma tushen shirye-shiryen da ya kafa a ma'aikatar.

Tsohon ministan ya kuma yi fatan alheri ga wanda ya maye gurbinsa tare da yi masa fatan samun nasara a nauyin da aka ɗora masa.

"Duk da yake ban ɗauki lokaci mai tsawo ba, ina alfahari da ci gaban da muka samu da kuma ginin da muka yi. Ina taya minista mai jiran gado murna da fatan samun nasara. Ina da yaƙinin za su ɗora kan nasarorin da muka samu."

Kara karanta wannan

Jerin sababbin ministocin da Tinubu ya nada da jihohin da aka dauko kowannensu

"Ga shugaba Tinubu, a matsayinsa na shugabana, ina yi wa gwamnatinsa fatan alheri don ci gaba da samun nasara."

- Abdullahi T. Gwarzo

Tinubu ya maye gurbin Betta Edu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya maye gurbin Betta Edu, dakatacciyar ministar harkokin jin ƙai da yaye talauci.

Shugaban ƙasar ya naɗa Dr Nentawe Yilwatda a matsayin sabon ministan jin ƙai, wanda zai maye gurbin Betta Edo bayan dogon lokaci da dakatar da ita.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng