Rusa Ma'aikatar da Yar'adua Ya Kafa Ta Jawowa Shugaba Tinubu Suka

Rusa Ma'aikatar da Yar'adua Ya Kafa Ta Jawowa Shugaba Tinubu Suka

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sauye sauye a zaman majalisar zartarwa na ranar Laraba, 23 ga watan Oktoba
  • Daga cikin gyaran da Bola Tinubu ya yi akwai sauya sunan ma'aikatar yankin Neja Delta da shugaba Umaru Musa Yar'adua ya kafa
  • Yan siyasa da shugabannin Neja Delta sun bayyana ra'ayoyi mabanbanta kan hukuncin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mutanen yankin Neja Delta sun bayyana ra'ayoyi mabanbanta kan zargin rusa ma'aikatarsu da Bola Tinubu ya yi.

Shugaba Tinubu ya dauki matakin canza sunan ma'aikatar Neja Delta zuwa ma'aikatar yankunan Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Dalilin Bola Tinubu na korar ministoci 5 ya bayyana, an faɗi asalin abin da ya faru

Bola Tinubu
Yan Neja Delta sun soki Tinubu kan sauya sunan ma'aikatarsu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Vanguard ta haɗa rahoto kan yadda mutanen Neja Delta suka bayyana ra'ayoyi kan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Minista: Ba a rusa ma'aikatar Neja Delta ba

Bayan fara ce-ce-ku-ce kan lamarin, tsohon ministan ma'aikatar Neja Delta ya ce ba rusa ta aka yi ba.

The Guardian ta wallafa cewa Abubakar Momoh ya bayyana cewa har yanzu ma'aikatar za ta cigaba da aiki kawai an kara mata nauyi ne daga sauran yankunan Najeriya.

Ba amfanin sauya suna inji Omare

Wani shugaban matasa a Neja Delta, Eric Omare ya ce ba wani amfani wajen sauyawa ma'aikatar suna kwata kwata.

Eric Omare ya bayyana cewa sauya sunan zai rage amfani na musamman da ake kafa ma'aikatar domin shi.

A nasa bangaren, Edwin Clark ya bayyana cewa shugaba Yar'adua ya kafa ma'aikatar ne domin magance matsalolinsu kuma ba za su yarda da mayar da ita ta yankuna ba.

Kara karanta wannan

Jam'iyyu sun haɗu sun ragargaji Tinubu kan korar ministoci

Joseph ya yi madalla da rusa ma'aikatar

Wani dan jihar Bayelsa, Ambakederimo Joseph ya nuna farin ciki kan 'rusa' ma'aikatar Neja Delta da shugaba Bola Tinubu ya yi.

Joseph ya bayyana cewa dama ya kamata tun da dadewa a rusa ma'aikatar saboda cin hanci da rashawa da ya yawaita a cikinta.

An soki Tinubu kan korar ministoci

A wani rahoton, mun ruwaito muku cewa yan siyasa a Najeriya sun soki shugaban kasa Bola Tinubu kan korar wasu ministoci.

Jam'iyyun adawa a Najeriya sun ce lamarin ba zai kawo sauyin matsalar tattalin arziki ba wanda ita ce babbar damuwar da yan kasa ke fuskanta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng