Jerin Sababbin Ministocin da Tinubu Ya Nada da Jihohin da Aka Dauko Kowannensu

Jerin Sababbin Ministocin da Tinubu Ya Nada da Jihohin da Aka Dauko Kowannensu

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa majalisar ministocinsa garambawul.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Shugaba Tinubu ya naɗa sababbin ministoci guda bakwai da za su yi aiki a gwamnatinsa.

Tinubu ya nada sababbin ministoco
Tinubu ya nada sababbin ministoci guda bakwai Hoto: Dr Jumoke Oduwole, Muhammad Maigari Dingyadi, Dr Nentawe Yilwatda Goshwe
Asali: Facebook

Bola Tinubu ya yi garambawul

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya sanya a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙasan ya kuma sallami ministoci biyar a cikin garambawul ɗin da ya yi a ranar Laraba, 23 ga watan Oktoban 2024.

Hakazalika Shugaba Bola Tinubu ya sauyawa ministoci 10 ma'aikatun da za su yi aiki.

Kara karanta wannan

Matawalle: Dalilin Tinubu na barin minista da ake zargi da "daukar nauyin 'yan bindiga"

Jerin sababbin ministocin Tinubu

Mun tattaro muku jerin sababbin ministocin da jihohin da suka fito.

1. Mohammed Maigari Dingyadi

Mohammed Maigari Dingyadi ya samu muƙamin ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Mohammed wanda ya fito daga jihar Sokoto ya riƙe muƙamin ministan harkokin ƴan sanda a gwamnatin Muhammadu Buhari.

Ya taɓa riƙe muƙamin sakataren gwamnatin jihar Sokoto kuma tsohon ɗan majalisar wakilai ne.

2. Idi Mukhtar Maiha

Idi Mukhtar Maiha ya samun muƙamin minista a sabuwar ma'aikatar da aka ƙirƙiro ta ci gaban kiwon dabbobi.

Idi Maiha wanda ya fito daga jihar Adamawa shi ne shugaban gidan gonan Zaidi Farms da ke Kaduna.

3. Nentawe Yilwatda

Shugaba Tinubu ya naɗa Nentawe Goshwe Yilwatda a matsayin ministan jinƙai da rage talauci, inda ya maye gurbin Betta Edu wacce aka kora.

Nentawe ya fito ne daga jihar Plateau. A shekarar 2023 ya yi takarar gwamnan jihar ƙarƙashin jam'iyyar APC inda ya yi rashin nasara a hannun Gwamna Caleb Mutfwang.

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya tura sako ga Tinubu awanni bayan raba shi da mukaminsa

4. Suwaiba Said Ahmed

Dr. Suwaiba Said Ahmed wacce ta fito daga Babura, jihar Jigawa ta samu muƙamin ƙaramar ministar ilmi.

Dr. Suwaiba lakcara ce a jami'ar Bayero (BUK) da ke Kano kuma darakta a cibiyar nazarin jinsi ta jami'ar.

5. Bianca Ojukwu

Bianca Odinakachukwu Olivia Odumegwu-Ojukwu ta samu muƙamin ƙaramar ministar harkokin waje.

Bianca wacce haifaffiyar jihar Anambra ce, ta kasance ƴar siyasa, lauya, ƴar kasuwa kuma matar tsohon ɗan gwagwarmayar kafa ƙasar Biafra, Odumegwu Ojukwu.

Ta taɓa riƙe muƙamin babbar mai ba shugaban ƙasa shawara ta musammam kan harkokin ƴan Najeriya da ke ƙasashen waje a gwamnatin Goodluck Jonathan.

A shekarar 2012 ta zama jakadan Najeriya zuwa ƙasar Ghana sannan daga bisani aka mayar da ita jakadan Najeriya a ƙasar Spain.

6. Jumoke Oduwole

Jumoke Oduwole wacce ta fito daga jihar Legas ta samu muƙamim ministar kasuwanci da zuba hannun jari.

Jumoke wacce lauya ce ta riƙe muƙamin mai ba da shawara ta musamman ga Tinubu kan zuba hannun jari.

Kara karanta wannan

Dalilin Bola Tinubu na korar ministoci 5 ya bayyana, an faɗi asalin abin da ya faru

7. Yusuf Abdullahi Ata

Yusuf Abdullahi Ata ya samu muƙamin ƙaramin ministan gidaje da raya birane inda ya maye gurbin Abdullahi T. Gwarzo.

Yusuf Abdullahi wanda ya fito daga Kano, ya taɓa riƙe muƙamin shugaban majalisar dokokin jihar.

Tinubu ya tura saƙo ga korarrun ministoci

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya godewa ministocin da ya kora daga aiki bisa gudummuwar da suka ba gwamnatinsa da ƙasa baki ɗaya.

Shugaban ƙasar ya yi masu fatan alheri a dukkan lamurran da za su sa a gaba, inda ya ce Najeriya ba za ta manta da hidimar da suka yi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng