Yan Bindiga Sun Shiga Uku, An Faɗi Abin da Gwamnonin Arewa 2 Suka Tattauna a Taron Abuja

Yan Bindiga Sun Shiga Uku, An Faɗi Abin da Gwamnonin Arewa 2 Suka Tattauna a Taron Abuja

  • Gwamnonin jihohin Zamfara da Katsina sun gana da ministan tsaro da mai ba da shawara kan tsaron ƙasa, Nuhu Ribadu
  • Mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, ya ce taron ya tattauna yadda za a haɗa karfi wajen dawo da zaman lafiya
  • Haka nan gwamnoni sun tattauna kan shawarwarin da gamayyar kungiyoyin Arewa, CNG suka gabar kan sha'anin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, da takwaransa na Katsina, Dikko Radda, sun yi ganawar sirri da ministan tsaro, Badaru Abubakar.

Bayan haka gwamnonin biyu sun kuma gana da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu.

Dikko Radda, Dauda da NSA, Badaru.
Gwamnonin Zamfara da Katsina sun gana da ministan tsaro da NSA Hoto: @AM_Saleem
Asali: Twitter

Tarukan guda biyu sun gudana ne ranar Talata, 22 ga watan Oktoba a ofishin NSA da ke hedkwatar tsaro a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

PDP ta amince Damagum ya sauka, za a bayyana sabon shugaban jam'iyya na ƙasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.

Abin da gwamnonin suka tattauna a Abuja

Ya ce tarukan biyu sun maida hankali ne kan shawarin da gamayyar kungiyoyin Arewa, CNG ta bayar game da yadda za a tunkari matsalar tsaro a Arewa.

"A jiya talata Gwamna Dauda Lawal na Zamfara da Dikko Radda na Katsina suka gana da ministan tsaro Badaru Abubakar a Abuja.
"Sun tattauna kan abin da ya shafi tsaro da haɗa karfi wajen magance matsalar.
"Bayan wannan taron ne gwamnoni suka ƙarasa ofishin NSA Nuhu Ribadu inda suka ƙara wani zaman duk a kan matsalar tsaro."
"Taron da suka yi a ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro ya duba tare da amincewa da shawarwarin da CNG ta gabatar dangane da hanyoyin samar da tsaro."

Kara karanta wannan

Damagum: Gwamna a Arewa ya yi amai ya lashe kan shugabancin PDP na ƙasa

Gwamnonin sun amince da shawarin CNG

Sanarwar ta ce CNG ta samu wakilcin shugaban kwamitin amintattu, Nastura Ashiru Shariff da shugaban kwamitin tsaron ƙungiyar, Alhaji Bashir Yusuf..

Ana ganin amincewa da shawarwarin CNG wani babban yunkuri ne na magance matsalolin rashin tsaro da ke addabar Arewacin Najeriya.

"Bana tsoron EFCC" - gwamna Dauda Lawal

A wani rahoton kuma Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ko kaɗan ba ya tsoron hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC).

Gwamnan ya bayyana cewa ya kamata waɗanɗa aka ba ragamar jagorancin al'umma su kasance masu gaskiya da riƙon amana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262