Jerin Kananan Ministoci da Suka Koma Manya bayan Tinubu Ya Yi Garambawul
- Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi sauye-sauye a mukaman Ministoci a gwamnatinsa bayan watanni ana jira
- Tinubu ya sallami wasu Ministoci biyar daga gwamnatinsa yayin da ake kiraye-kiraye kan korar wasu daga cikinsu
- Bayan sallamar Ministocin, Tinubu ya kuma amince da nadin sababbi domin maye gurbinsu da kuma hade wasu ma'aikatu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya sallami wasu Ministoci biyar inda ya amince da nadin wasu guda bakwai a yau Laraba 23 ga watan Oktoban 2024.
Fadar shugaban kasar ta ruwaito cewa shugaban ya karawa wasu ƙananan Ministoci zuwa manya a ma'aikatu daban-daban.
Daily Trust ta tabbatar da cewa shugaban ya yi sauye-sauye a ma'aikatu bayan hade wasu daga cikinsu wanda ya tilasta sallamar Ministocin guda biyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministocin da aka karawa matsayi
Legit Hausa ta duba Ministocin da suka samu karin girma daga matsayinsu zuwa manyan Ministoci.
1. Morufu Alausa - Ministan Ilimi
Bola Tinubu ya daga matakin Alausa daga karamin Ministan lafiya zuwa babban Minista a ma'aikatar Ilimi.
Nadin Alausa ya biyo bayan sallamar Farfesa Tahir Mamman daga mukaminsa a yau Laraba 23 ga watan Oktoban 2024.
2. Imaan Sulaiman-ibrahim - Ministar mata
Imaan Sulaiman-ibrahim ta maye gurbin tsohuwar Ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye a yau Laraba.
Kafin nadin nata, Imaan wacce ta fito daga jihar Nasarawa ita ce karamar Ministar harkokin yan sanda a Najeriya.
3. Ayodele Olawande - Ministan cigaban matasa
Ayodele Olawande ya samu karin girma zuwa muƙamin babban Ministan cigaban matasa a yau Laraba 23 ga watan Oktoban 2024.
Kafin wannan nadin, Olawande ya kasance karamin Minista a ma'aikatar cigaban matasa inda ya zama babban Minista.
Tinubu ya yi garambawul a gwamnatinsa
A baya, kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya rushe wasu ma'aikatu a Najeriya tare da yin sauye-sauye a mukaman Ministoci.
Bola Tinubu ya rushe ma'aikatar harkokin wasanni da kuma Neja Delta inda ya hade wasu ma'aikatu daban-daban a kasar.
Wannan na zuwa ne bayan korafe-korafe da yan Najeriya suka rika yi domin shugaban ya sallami wasu daga cikin Ministocinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng