Bola Tinubu Ya Ɗauko Ministan Buhari, Ya Naɗa Shi a Muƙami Bayan Korar Ministoci
- Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Sunday Dare a matsayin mai ba da shawara kan harkokin sadarwa da wayar da kan jama'a
- Sunday Daye dai ya yi aiki a matsayin ministan matasa da bunkasa harkokin wasanni a gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
- Fadar shugaban ƙasa ce ta tabbatar da wannan naɗi a wata sanarwa ranar Laraba bayan korar ministoci biyar daga aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
State House, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya nada Sunday Dare a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin sadarwa da wayar da kan jama’a.
Sunday Dare, mai sarautar Agbaakin na Ogbomoso, ya yi aiki a matsayin ministan harkokin matasa da wasanni a gwamnatin Muhammadu Buhari.
Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da naɗin tsohon ministan a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, 23 ga watan Oktoba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Dare ya kasance kwararren ɗan jarida kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jaridar mako-mako ta The News and Tempo, sannan ya yi aiki a ƙasar Amurka.
An haife shi a ranar 29 ga Mayu, 1966. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria (ABU) inda ya karanci kwas din 'B.Sc International Studies."
Sannan ya yi digiri na biyu a Jami'ar Jos da ke jihar Filato kuma ya kammala da sakamako mafi daraja a fannin ilimin sanin doka watau Law.
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng