Shugaba Tinubu Ya Aika Muhimmin Saƙo ga Ministoci 5 da Ya Kora daga Aiki
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya aika sakon godiya da fatan alheri ga tsofaffin ministoci biyar da ya sallama daga aiki
- A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, Tinubu ya gode masu bisa aikin da suka yi wa ƙasa a tsawon lokacin da suke ofis
- Shugaban kasar ya kuma ja hankalin sababbin ministocin da ya naɗa cewa kyau su fahimci kudirin gwamnatinsa na kawo ci gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya godewa ministocin da ya kora daga aiki bisa gudummuwar da suka ba gwamnatinsa da ƙasa baki ɗaya.
Shugaban ƙasar ya yi masu fatan alheri a dukkan lamurran da za su sa a gaba, inda ya ce Najeriya ba za ta manta da hidimar da suka yi ba.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai taimaka shugaban kasa kan harkokin midiya, Dada Olusegun ya wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Bola Tinubu ya kori ministoci 5
Idan ba ku manta ba Tinubu ya sallami ministoci biyar daga aiki a garambawul din da ya yi a majalisar zartaswa ta ƙasa.
Waɗanda aka sallama sun haɗa da Ministan harkokin yawon buɗe ido, Lola Ade John, Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman da Ministar mata, Uju-Ken Ohanenye.
Sauran su ne ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Gwarzo da kuma Ministar matasa, Jamila Bio Ibrahim.
Sakon Tinubu ga korarrun ministoci da sababbi
Sanarwar ta ce:
"Shugaban ƙasa ya godewa ministoci masu barin gado bisa aikin da suka yi wa ƙasa, sannan yana masu fatan alheri a duk abin da suka sa a gaba."
Bayan haka Shugaba Tinubu ya bukaci sabbabin ministocin da ya naɗa da waɗanda ya sauyawa wurin aiki da su shirya yi wa ƙasa hidima.
Ya ƙara da cewa dole dukkan waɗanda aka naɗa su gane kokarin da gwamnati ke yi wajen ɗora Najeriya kan turbar ci gaba da mai ɗorewa.
Tinubu ya maye gurbin Betta Edu
A wani rahoton kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya maye gurbin Betta Edu, tsohuwar ministar harkokin jin kai da yaƙi da talauci a Najeriya.
Shugaban ƙasar ya amince da naɗin Dr Nentawe Yilwatda, ɗan asalin jihar Filato a matsayin sabon ministan jin ƙai.
Asali: Legit.ng