Bayan Korar Ministoci, Tinubu Ya Rantsar da Dan Arewa a Babban Muƙami

Bayan Korar Ministoci, Tinubu Ya Rantsar da Dan Arewa a Babban Muƙami

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sabon shugaban hukumar da'ar ma'aikata ta kasa a fadar shugaban kasa
  • Bayan Dr Abdullahi Usman Bello ya sha rantsuwa, ya yi alkawarin yin aiki da gaskiya ba tare da nuna sani ko sabo ba
  • A yayin zaman majalisar zartarwa na yau ne Bola Tinubu ya rantsar da Dr Bello bayan korar wasu ministoci daga aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya rantsar da sabon shugaban hukumar da'ar ma'aikata ta kasa (CCB).

An ruwaito cewa Bola Tinubu ya rantsar da Dr Abdullahi Usman Bello ne yayin zaman majalisar zartarwa a yau.

Kara karanta wannan

A karshe, Tinubu ya ji korafe korafen yan Najeriya, ya sallami Ministoci 5

Tinubu
An rantsar da shugaban CCB. Hoto: Aso Villa
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa wasu daga cikin yan majalisar zartarwa ba su samu halartar zaman yau ba saboda wasu ayyuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya rantsar da shugaban CCB

A yau Laraba, 23 ga watan Oktoba shugaba Bola Tinubu ya rantsar da shugaban hukumar da'ar ma'aikata ta kasa.

Bayan shan rantsuwa, Dr Abdullahi Usman Bello ya ce ya shirya tsaf domin ba maraɗa kunya dan gane da babban aikin da aka daura masa.

Aikin hukumar da'ar ma'aikata

Tribune ta wallafa cewa Dr Abdullahi Usman Bello ya bayyana cewa babban aikin hukumar CCB shi ne yaki da cin hanci da rashawa a ma'aikatu.

Sabon shugaban ya bayyana cewa CCB aka fara kafawa a Najeriya domin yaki da cin hanci da rashawa da tabbatar da hali na gari a tsakanin ma'aikata.

Shugaban CCB ya ce zai yi aiki tuƙuru

Kara karanta wannan

Ana dakon korar Ministoci, Tinubu ya rushe ma'aikatu, ya yi garambawul a gwamnati

Sabon shugaban hukumar CCB ya bayyana cewa zai tabbatar da yaki da rashawa duk da cewa abu ne mai wahala a Najeriya.

Dr Abdullahi Usman Bello ya mika godiya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan ba shi muƙamin da ya yi.

Bola Tinubu ya kori ministoci 5

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kori ministoci biyar yayin zaman majalisar zartarwa na yau.

Hakan na zuwa ne bayan yadda yan Najeriya suka yawaita kira ga Bola Tinubu kan canza wasu daga cikin jami'an gwamnatinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng