"Akwai Matsala": Shugaban Majalisa Ya Faɗi Yara Miliyan 20 da Ka Iya Zama Ƴan Bindiga
- Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya ce yawan yaran da ba su zuwa makaranta babbar matsala ce ga kowace ƙasa
- Akpabio ya ce yara miliyan 20 da ke gararamba a tituna a Najeriya na iya zama ƴan bindiga nan gaba idan ba a ɗauki mataki ba
- Barau Jibrin ya ce adadin ya yi yawa kuma idan ba a ɗauki mataki ba matsalar da za su haifar sai ta shafi kowa musamman a Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban majalisar dattawan Najeriya ya nuna danuwa kan yawan ƙananan yara masu gararamba a gari waɗanda ba su zuwa makaranta.
Sanata Godswill Akpabio ya ce alkaluma sun nuna akwai yara miliyan 20 da ba su zuwa makaranta a faɗin ƙasar nan, yana mai cewa za su iya zama ƴan bindiga nan gaba.
Yara za su iya zama matsala nan gaba
Akpabio ya bayyana haka ne a zaman ƴan majalisar dattawa na yau Laraba, 23 ga watan Oktoba, 2024, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake tsokaci yayin muhawara kan yaran da ba su zuwa makaranta, Akpabio ya ce idan ba a tashi tsaye ba za su iya shiga ayyukan laifi.
Sanatoci sun yi muhawara kan lamarin ne bayan shugaban kwamitin ilimin Firamare da Sakandire, Usman Lawal Adamu (Kaduna ta Tsakiya) ya gabatar da rahoto.
Sanata Akpabio ya hango matsala
Sanata Akpabio ya ce ƙaruwar yaran da ba su zuwa makaranta babban haɗari ne ga sha'anin tsaron ƙasar nan.
"Ƙananan yara miliyan 20 ba ba su zuwa makaranta illa ce babba ga kowace ƙasa, za su iya zama ƴan bindiga, wannan babban haɗari ne a ƙasar nan.
"Don haka wannan babban lamari ne. Wannan shi ne ya jawo rashin tsaro a kasar nan,” in ji Akpabio.
"Abin sai ya fi taɓa Arewa" - Barau Jibrin
A nasa jawabin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya ce wannan babbar matsala ce da ya kamata a tashi tsaye domin magance ta.
Barau ya ce:
"Idan muka yi sakaci da wannan, to tamkar mun dasa wa kanmu bam ne, da zaran ya fashe sai ya shafi kowa musamman Arewacin Najeriya.
“Akwai buƙatar daƙile yawaitar yaran da ke yawo a tituna ba tare da zuwa makaranta ba, matsala ce babba ba wai ga gwamnati kaɗai ba, kowa zai ba da gudummuwa."
Majalisa na shirin raba jihar Oyo
A wani rahoton kuma kun ji majalisar wakilai ta fara yunkurin kirkiro sabuwar jiha a Najeriya inda take shirin raba Oyo zuwa jihohi biyu, Ibadan da Oyo.
Honarabul Akeem Adeyemi da wasu ‘yan majalisu ne suka dauki nauyin kudirin, sun nemi a kafa jihar Ibadan da Ibadan a matsayin babban birni.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng