An Zo Wurin: Kotu Ta Yi Zama kan Zargin Ganduje da Almundahana, Ta Shirya Yanke Hukunci
- Yayin da ake shari'a kan zargin shugaban APC, Abdullahi Ganduje da cin hanci, kotu ya shirya yanke hukunci
- Babbar kotun jihar Kano ta sanya 20 ga watan Nuwambar 2024 a matsayin ranar raba gardama kan dukkan zargin
- Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin Ganduje da matarsa da wasu mutane kan karkatar da biliyoyin kuɗi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Babbar kotun jihar Kano ta shirya kawo karshen korafi da zargi a kan shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje.
Kotun ta sanya ranar 20 ga watan Nuwambar 2024 domin yanke hukunci kan zargin Ganduje da cin hanci da almundahana da dukiyar al'umma.
Kotu za ta raba gardama kan zargin Ganduje
Channels TV ta tabbatar da cewa ana zargin Ganduje da karkatar da biliyoyin Naira lokacin da yake mulki a jihar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana tuhumar Abdullahi Ganduje da matarsa, Hafsat Umar da mutane uku da kuma wasu kamfanoni uku kan laifuffuka takwas.
An koma kotu domin shari'ar Ganduje
Yayin zamanta a yau Laraba 23 ga watan Oktoban 2024, kotun ta shirya sauraran korafe-korafen daga mutane shida da ake zargi.
Lauyan wadanda ke kara, Adeola Adedipe ya ce a shirye suke domin cigaba da shari'ar da ake yi.
Ya ce akwai wani da zai ba da shaida kan shari'ar ya taso daga Lagos musamman saboda korafin da ake yi na cin hanci.
Lauyoyin wadanda ake zargi sun roki kotu
Sai dai lauyan wadanda ake zargi, Offiong Offiong ya bukaci karin lokaci domin samun damar duba korafe-korafen da ake yi musu.
Mai shari'a, Amina Adamu Aliyu ta yi tatali da bukatar yanke hukunci da wadanda ke kara suka yi inda ta dage zaman zuwa ranar 20 ga watan Nuwambar 2024.
Ganduje ya fadi wanda ya ceci APC
Kun ji cewa shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya yabawa Abdulkareem Abubakar Kana wajen bikin da aka shirya domin karrama shi.
Shugaban APC na kasa ya ce mai ba jam’iyyar shawara a kan shari’a ya taka rawar gani wajen hana su rasa N1.5bn.
Farfesa Abdulkareem Abubakar Kana wanda ya na cikin majalisar NWC a jam'iyyar APC ya samu karin matsayi ne zuwa SAN.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng