Abba Ya Kaddamar da Wata Hanya cikin Dare, Ya Fadi Muhimmancin Aikin
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da wata hanya a karamar hukumar Tofa a daren ranar Talata
- Abba Kabir Yusuf ya bayyana dalilan da suka sanya shi tafiya zuwa kauyuka domin yin ayyuka a irin wannan lokaci
- Haka zalika gwamnan ya yi godiya ta musamman ga mutanen a kan yadda suka tarbi tawagarsa cikin girmamawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da muhimmiyar hanya a karamar hukumar Tofa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da aikin hanyar ne a daren ranar Talata kamar yadda rahotanni suka nuna.
Legit ta tattaro bayanan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba ya kaddamar da hanya cikin dare
Abba Kabir Yusuf ya dauki tawaga mai ƙarfi domin ƙaddamar da aikin titi a karamar hukumar Tofa.
Gwamnan ya kaddamar da hanya mai nisan kilo mita biyar tare da sanya mata wuta mai amfani da hasken rana.
Amfanin hanyar da Abba ya kaddamar
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa yin titin na cikin ayyukan da ya dauko domin raya karkara.
A karkashin haka, gwamnan ya ce aikin zai taimaka wajen rage yawan masu tahowa birane daga karkara a jihar.
Sannan ya bayyana cewa wuta mai amfani da hasken rana da aka samar za ta bunkasa harkar kasuwanci a Tofa.
Abba ya yi godiya ga mutanen Tofa
Abba Kabir Yusuf ya mika godiya ga daukacin mutanen ƙaramar hukumar Tofa bisa tarbar da suka yi wa tawagarsa.
Gwamna ya kuma mika godiya ga Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe wanda shi ne wakilin Tofa a majalisar wakilai ta kasa.
Gwamnatin Abba za ta tura ɗalibai kasar waje
A wani rahoton, kun ji cewa Abba Kabir Yusuf ya fara shirin daukar dalibai domin zuwa karatu kasashen waje kamar yadda aka yi a baya.
Gwamnan ya fitar da sanarwar ne yayin karɓar daliban jihar Kano da suka dawo Najeriya bayan kammala digiri na biyu a kasar Indiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng