"Ba Mu Son Hayaniya": Gwamma Ya Rufe Masallatai da Majami'u Sama da 300

"Ba Mu Son Hayaniya": Gwamma Ya Rufe Masallatai da Majami'u Sama da 300

  • Gwamnatin Legas ta ce a shekarar da ta gabata kaɗai ta rufe Masallatai, Majami'u da wasu wurare saboda yawan hayaniya
  • Shugaban hukumar kare muhalli, Dr. Babatunde Ajayi ya ce tun farko sun gargaɗi shugabannin addinai kan cika ƙarar lasifika
  • Ya ce da farko mutane sun yi biyayya, amma daga bisani suka yi kunnen ƙashi wanda ya sa jami'an gwamnati ɗaukar mataki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Legas - Gwamnatin Legas ƙarƙashin jagorancin Gwamna Babajide Sanwo-Olu ta ce ta rufe wurare 352 saboda yawan hayaniya a shekarar da ta gabata a faɗin jihar.

Daga cikin wuraren da gwamnatin ta tabbatar da rufewa har da Masallatai da coci-coci, wuraren ibadar Musulmai da Kiristoci.

Kara karanta wannan

Minista ya shiga matsala, an buƙaci Shugaba Tinubu ya kore shi daga aiki nan take

Gwamma Babajide Sanwo-Olu.
Gwamnatin Legas ta rufe masallatai da coci coci saboda damun mutane da hayaniya Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Asali: Twitter

Vanguard ta ruwaito cewa babban manajan hukumar kare muhalli ta jihar Legas, LASEPA, Dr Babatunde Ajayi, ne ya bayyana haka a ofishinsa da ke Ikeja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin rufe masallatai da coci a Legas

Da yake ba da rahoton ayyukan da suka yi a bara, shugaban LASEPA ya ce sun rufe masallatai, coci-coci da wasu wurare da dama saboda sun karya dokar sauti.

Dr. Ajayi ya ce mutane sun lalace da rashin jin magana da ƙa'idoji musamman game da matsalar hayaniya ta hanyar kunna lasifiƙa ko kaɗe-kaɗe da sautin da ya wuce ƙima.

"Matsalar da muka fuskanta bayan dokar hana kunna abubuwan hayaniya shi ne taurin kan mutane, da farko sun fara biyayya ga dokar, amma daga bisani suka ci gaba da harkokinsu.
"Daga nan mu kuma muka fara aikinmu na tabbatar da bin doka da oda, tarar da muke cin mutane da kuma rufe wurare da ke tada hayaniya ya sa suka dawo suka saduda."

Kara karanta wannan

NDLEA: Majalisa ta dauki mataki kan zargin kama kwayoyi a gidan sanata

- Dr Babatunde Ajayi.

Gwamnatin Legas ta gargaɗi mutane tun farko

Shugaban LASEPA ya ce tun farko sun zauna da wakilan addinai musamman kiristoci, waɗanda suke fito da lasifika a cikin jama'a suna wa'azi.

A cewarsa, gwamnati ta gargaɗe su kan ƙaro sautin da ya wuce ƙima, wanda hakan ka iya takurawa wasu amma duk da haka wasu ba su ji ba.

Fasto ya hango za a yi girgizar ƙasa a Legas

A wani rahoton kuma fitaccen malamin nan, Primate Elijah Ayodele, ya ce nan ba da dadewa ba 'yan Legas za su fuskanci karamar girgizar kasa.

A wani sabon faifan bidiyo da Legit Hausa ta gani, malamin ya roki al’ummar Legas da su dage da addu’a a kan girgizar kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262